Ya kasa samun aiki saboda yana da fuskar yara

Wani mai shekara 27 a garin Dongguan a ƙasar Chana yana shan fama wajen neman aiki, saboda fuskarsa tana nuna ta bai kai shekara 20 ba.

Matashin mai suna Mao Sheng, ana yi masa kallon ƙaramin yaro da shekarunsa suka gaza ya samu aiki.

Duk lokacin da matashin ya ce, ya kai shekara 27, mutane ba su yarda da hakan, inda suke yi masa kallon bai wuce shekara 10 ba.

Sai dai yayin da wasu suke ganin hakan a matsayin wata albarka ce, saurayin yana ganin cewa ana aibanta shi, tunda hakan ya hana shi samun aiki.

Yawancin masu ɗaukar ma’aikata ba su yarda cewa ya kai shekarun da ya ke ikirarin ya kai ba, kuma sukan ce ba za su ɗauke shi aiki ba don kada hukumomi su zarge su da sa ƙananan yara aiki saboda kallon shekarun ƙuruciyar da ake yi masa.

Mao Sheng, ya ɗauki hankalin jama’a a ƙasar China a makonnin da suka gabata, bayan wani bidiyo da aka ɗauka a kan titunan Dongguan da ya bazu a kafar sadarwa ta Douyin a manhajar TikTok.

A cikin bidiyon, matashin ya bayyana shekarunsa kuma ya yi ƙorafin cewa, ya kasa samun aikin da zai tallafa wa mahaifinsa, wanda ke samun sauƙi daga ciwon varayin jiki.

Ya ce, ya nemi aiki a masana’antun garinsu tare da abokansa, amma yayin da su suka samu aiki nan ta ke, shi bai yin sa’a a ɗauke shi ba saboda don kamanninsa.

Labarin Sheng ya tava zukatan miliyoyin mutane a Chana, waɗanda da yawa daga cikinsu suka zargi masu ɗaukar aiki da ƙin ba matashin dama saboda fuskar yara da ya ke da ita.

An yi sa’a, bayan labarinsa ya shahara wasu ’yan kasuwa da dama sun tuntuve shi suka ba shi ayyukan yi.

Wani faifan bidiyo da aka wallafa a kafar Douyin kwanaki kaɗan da suka gabata ya nuna cewa, Mao ya amince da ɗaya daga cikin ayyukan da aka yi masa ta yi, kuma yana fatar samun kuɗin da zai taimaka wa mahaifinsa ya murmure.

Kuma da zarar mahaifin ya murmure shi kuma yana fata ya samu budurwa da zai aura don kafa nasa iyalin.

Duk da an ɗauki labarin Mao Sheng a gidajen labarai da yawa a ƙasar China, babu ɗaya daga cikinsu da ya ambaci dalilin da fuskar matashin ta zamo haka.

Akwai masu zargin cewa dole akwai alaqar halittar da take haɗe da kwakwalwa wacce ta ke sa girman jikin mutum, wanda ke sarrafa girman jiki.

Saboda an ga irin waɗannan a baya, inda manya mutane suke da jikin yara, kuma irin wannan halittar ce kusan koyaushe ta ke haddasa haka.