Hanyoyin magance zargi a zaman aure

Cigaba daga makon jiya

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkanmu da saduwa a wani sabon makon a filinmu na Zamantakewa na jaridarku mai farin jini, Manhaja. Za mu cigaba daga inda muka tsaya a maudu’inmu na makon da ya gabata. Inda muka bayyana wa masu karatu ma’anar zargi a gidan aure da kuma abubuwan da suke jawo zargi a zaman aure da suka haɗa da: kishi mai tsanani, rashin yarda da kai, rashin fahimtar juna, rashin soyayya, aikata mugayen laifuka a ɓoye, rashin ƙauna, buɗe ƙofar zargi, da sauransu. A wannan mako za mu cigaba. Sannan za mu kawo muku bayanai a game da illolin da zargi yake haifarwa a gidan aure, da kuma hanyoyin da za a bi don a magance zargi a zaman aure. A sha karatu lafiya.

Illolin da zargi kan haifar a gidan aure
Kamar yadda na faɗa a makon da ya gabata, zaman aure fa ba ya tava yiwuwa ba yarda a tsakanin ma’aurata. Hasali ma ita yarda da juna ita ce babbar ginshiƙi daga cikin ginshiƙan da suke riƙe da aure. Daga ranar da zargi ya shigo kuma, to fa akwai matsala. Domin gida ya birkice kenan ba zama lafiya.

Babbar matsalar da zargi yake fara haifarwa ga ma’aurata shi ne, idan wanda ake zargin ya gano cewa, ana zarginsa. Ku sani zargi yana da ciwo. Da wuya a dinga zargin mutum, kuma ya gano hakan, kuma ya haƙura ba tare da ya ɗauki mataki a kai ba.

Da farko, zargi na haifar da rashin yarda a tsakanin ma’aurata. Daga lokacin da ɗaya daga cikin ma’aurata ya gano cewa ɗayan yana zarginsa, to fa an shata layin daga. Domin kamar yadda na faɗa, wanda ake zargi ba zai taɓa farin ciki da hakan ba.

Abinda muka sani dai shi ne, ma fi yawan zargi a zaman aure maza ne suka fi yinsa. Matan ma suna yi, amma sun fi yi a kan zargin mijinsu yana kula wasu mata a waje. Ko zargin yana fifita kishiya ko danginsa a kanta.

Amma shi zargin namiji ya fi muni da illa a cikin gidan aure. Domin shi ne mai wuƙa da nama. Rashin samun nutsuwar zuciyarsa zai haifar da rashin kwanciyar hankali a zaman auren bakiɗaya. Wasu ƙarin illolin da zargi yake jawowa a gidan aure sun haɗa da:

Idan mace ta gano namiji yana zarginta za ta ji ƙiyayyarsa a zuciyarta. Sannan girma da ƙimarsa zai ragu sosai a zuciyarta. To aure babu so da girmamawa, ina labari?

Hakazalika, sa wa abokin zama ido da takura masa da bincike shi ma yana sa ya ji kun fita daga ransu. Ita soyayta ita ma dangin goro ce tana buƙatar a ɗan sarara. Sannan ba a mata dole. Ba wa abokin zama ‘yanci da damar sararawa yana daga cikin abubuwan da suke ƙara yauƙaƙa soyayya. Ka takure ta ka ce kada ta fita, shi ma wannan bai kamata ba. Wani ko gidansu ba ya ƙaunar ta je saboda kawai yana gudun kada wasu mazan su ganta a hanya ko mazan gidansu ƙanne ko yayyenta kishi yake yi.

Sannan bibiyar matarka ko mijinki don kuna zarginsu zai sa ku gano wani mugun abin da zai kawo cikas a aurenku. Misali mace mai duba wayar miji. Akwai wani Malami da ya faɗa cewa, daga ranar da mace ta fara duba wayar miji, to ta fara ƙirge. Aurenta na gab da mutuwa.

Sannan wani abun kuma, kamar yadda na faɗa a baya, yarda na cikin ginshiƙan aure. Daga ranar da abokin zama ya gano ana zarginsa saboda wasu abubuwa da ya yi ko ya faɗa a labari, wasu abubuwan ma bai san abin zargi ba ne. Amma saboda ɗabi’ar zargi ta abokin zaman, sai a fassara shi ko ita. Don haka a gaba, ya daina sakin jiki kenan da abokin rayuwa.

Gudun kada ya yi wata magana ko ya yi wani abu a fassara shi. Don haka, yarda da sakin jiki tsakanin ma’auratan ya ƙaura.
Sannan abu na gaba kuma, idan ana zargin mutum da ma a rayuwa, sai ya zama mai ɓoye-ɓoyen sirrinsa daga wanda yake zargin nasa. Misali, idan mace tana takura wa namiji da zargin yana wasu abubuwa da kuɗi, zai iya fara ɓoye mata samunsa. Ko idan zai yi wa danginsa abu ya dinga ɓoye mata.

Haka zargin mutum yana sa ya shiga cikin wasu muggan ɗabi’u kamar shaye-shaye da sauransu don kawar da damuwarsa. Wata matar ma idan ba mai tsoron Allah ba ce, sai ta fara kula wasu mazan don samun sassaucin damuwa. Kuma duk bincikenka ka kasa ganowa. Ko kuma ma idan ka gani ɗin ma ita ko a jikinta tunda girmanka da ƙimarka sun zube a idanunta.

Zargi da takura wa matarka zai iya haifar mata da damuwa mai tsanani. Saboda zargi yana da ciwo ƙwarai ga wanda ake yi wa. Kuma yawan damuwa zai iya haifar da cutuka mugga kamar hawan jini ko cutar damuwa.

Shi kansa mai zargin zai iya haɗuwa da waɗancan cututtuka da na zano a sama. Domin su ma na samunsu a sanadiyyar damuwa da tashin hankali. Shi kuwa mai zargin iyalinsa ba za a gaya masa tashin hankali ba gami da rashin nutsuwar rai. Saboda kullum a cikin fargabar kada zarginka kan mata ko miji ya tabbata. Kuma kada bincikenka ya jawo allura ta tono garma.

Hanyoyin magance zargi tsakanin ma’aurata:

Abu na farko shi ne, ka fawwala wa Allah komai. Ka zama mai kyaun zuciya. Idan har ka yarda ba ka aikata mugun abu, to me ya sa za ka zargi wani yana yi? Idan har abokin rayuwarku yana ha’intarku a bayan idonku, to kuwa Allah zai bayyana muku ko ba daɗe, ko ba jima. Dabararku ba za ta sa ku gano ba idan Allah bai amince ba.

Sannan abu na biyu, a daina ɓoye-ɓoye ga juna. Shi ma yana ƙara iza wutar rashin zaman lafiya da zargi a gidajen aurenku. Duk da dai akwai wasu abubuwan da dole sai an ɓoye ga abokan rayuwa, saboda gudun fitina. Amma manyan abubuwa kamar idan ya ba ki kuɗin siyayya ki yi masa bayani zai ji ya gamsu ya rage zargi. Haka idan aure kake nufin ƙarawa, ka zaunar da ita ka yi mata bayani ba ƙumbiya-ƙumbiya ba.

Sannan yana da kyau a gano wai ina matsalar take? Gano matsala kowacce iri ce yana sa a samo maslahar yadda za a warware ta. Don haka idan ma’aurata suka gano abinda yake jawo musu zargi, suka magance shi sai a zauna lafiya. Dalilan zargi sun haɗa da, ƙarya, rashin cika alƙawari ko rashin kamun kai ga mace, ko zafin kishin mace ko namiji, da sauransu. Idan aka gano meye naku, sai ku gyara hali. Kuma a tuba kada a koma ruwa.

Sannan kuma wanda yake zargin yana da kyau ya ba da haƙuri in dai an samu cewa, zargin ba gaskiya ba ne. A cire girman kai a yi abinda ya dace. Su kuma waɗanda ake zargi, idan har tuban nasa ba tuban muzuru ba ne, an tabbatar da gaske yake to a yafe masa. Allah yana son masu yafiya.

Kuma a sani, da ma ita rayuwar aure ba wai rana guda ake samun fahimtar juna mai ɗorewa ba. Sai an gogu an kai ruwa rana. Rayuwar aure kamar yaron da aka haifa yau ne. Ba zai yiwu ya fara tafiya daga haihuwa ba. Amma sai ya iya zama, rarrafe, ta-ta-ta kafin ya fara tafiya. Don haka sai an yi haƙuri da juna, da kuma yi wa juna uzuri kafin a samu zaman lafiya mai ɗorewa.

Amma idan an yi yafiyar abu ya ci tura, to rabuwa da mace ko miji mai zargi shi ya fi. Domin wasu ɗabi’arsu ce zargi da zazzafan kishi. Musamman idan iyaye da sauran abokai sun kasa shawi kan matsalar. Sannan kuma mutum mai zargi ko zazzafan kishi zai iya hallaka abokin zamansa. Mun ga waɗannan matsaloli da dama a Kano. Inda mata sukan kashe miji ko kishiya saboda zargi.

Haka ko kes ɗin Maryam Sanda ai a kan zargi ne. Tana zargin mijinta da neman mata, kuma tana da tsananin kishi ta kashe shi har lahira.

Don haka, miji ko mata masu zargi abin tsoro ne. Sai ku nesanta da su, in dai ba su da niyyar dainawa. Don ba kowa yake tsoron Allah ba. Ga shaiɗan yana buga musu gangarsa mai zaƙin tsiya.

Haka ana buƙatar ma’aurata su zaunar da abokin rayuwa su tattauna a game da zargi. Misali, idan miji ya fiye zargi da quntata mace, za ta iya yi masa magana a lumana a kan ba ta jin daɗin zargin da yake yi. Idan ta kama ma har da wa’azi a kan abinda Allah da manzonsa suka ce. Sam kada a tunkare su da fushi a yi musu dai bayani. Domin za su qara tabbatar da abinda yake ransu. Daga nan zargin ya haura na da.

Wani lokacin maganar tana sa a samu lada. Don za a fitar da abokin zama daga ƙangin zargi. Domin wataƙila yana zargi ne a kan wani abu da ya jahilta. To amma sai a tattaunawar aka fitar da shi a duhu.

A nan za mu dakata, sai mako mai zuwa idan mai duka ya kai rai. Ina godiya da jinjina ga maranta. Allah ya bar zumunci.