Ya shekara 56 yana hawan keken da ya saya naira shida

Dga WAKILINMU

Malam Garba Nayamma ya kwashe shekaru 56 yana tuƙa keken da ya saya a zamanin tsohon shugaban ƙasar Nijeriya, Yakubu Gowon.

Ya ce, “ma sayi wannan keken ne fam uku wato naira shida kenan kuma har yanzu sai dai kawai idan wani abu ya lalace na sauya.”

Malam Garba ya ce, a tsawon shekarun nan da ya kwashe yana amfani da keken, da shi ya ke zuwa gona da ma duk wata ziyara da ya ke yi a garuruwan Arewacin Nijeriya.

“Duk yawon ‘yan matanci da muka yi da wannan keken muka yi shi. Na kan ɗauki abokaina domin zuwa zance inda na ke ɗora ɗaya a gaba sannan ɗaya kuma a kan kariya.”

Ya ƙara da cewa, a duk lokacin da aka ɗauke min wannan keken to lallai an taƙaita ni kasancewar shi ne abin hawana da na riga na sani.

Duk da cewa malam Garba ya tsufa domin ya wuce shekara 70 da haihuwa amma da kwarinsa wataƙila saboda irin shekarun da ya kwashe yana tuƙa wannan keke wanda hakan motsa jiki.

“Ba ni da wata cutar da ke damu na,” inji Malam Garba.