Fim ɗin ‘Wani Gari’ ne ya tada min da tsimin son harkar fim – Zulai Uwa ta Gari

“Mujallar Fim ce ubangidana a Kannywood”

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Hajiya Zulaihat Abdullahi Bebeji da aka fi sani da Uwa ta Gari ko Attajira, jaruma ce da mafi yawan finafinta a uwa ta ke fitowa. Ta shafe aƙalla kusan shekara 20 a masana’atar fim ta Kannywood. A hirarta da Ibrahim Hamisu a Kano, za ku ji tarihinta da irin gwagwarmayar da ta sha har zuwa wannan lokaci. Ku biyo mu:

BLUEPRINT MANHAJA: Da wa muke tare?

HAJIYA ZULAIHATU: Sunana Zulaihatu Aliyu Abdullahi Bebeji, ana yi min laƙabi da Hajiya Zulai Bebeji ko Hajiya Zulai Uwa ta Gari, a yanzu kuma anfi kirana da Attajira.

Za mu so ki ba mu taƙaitaccen tarihinki?

An haife ni a ƙaramar Hukumar Bebeji a shekarar 1975. Na taso a unguwar Birget da ke cikin birnin Kano. Na yi Islamiyya, sannan na yi makarantar primary ta Turaki Memorial College, sannan na yi sakandire a makarantar marigayi Garba Babanladi, sai aka yi min aure. A halin yanzu Ina zaune a Unguwar Charanchi da ke ƙaramar Hukumar Kumbotso, Kano.

Yaushe kika fara fito wa a finafinan Kannywood?

Na fara fito wa a fim a shekara 2002, to daga nan sai na yi aure, na tafi hutu sai a shekara ta 2011, wato shekara 11 kenan da dawowata masana’atar fim ta Kannywood.

Da wane fim kika fara?

Na fara da wani fim mai su na ‘Ƙudura’ na wanda marigayi Tijjani Harris ya bada umurni. Allahu Akbar! Ba zan tava mantawa da wannan fim ɗin ba, domin daraktan da na je na samu labarin ya riga ni zuwa maimakon ni zan riga labarin zuwa, Ina zuwa kawai aka sanya ni, a lokacin na fito a matar Sani Mai Iska, kuma tun da na fara harkar fim kusan da Ali Nuhu na ke fitowa. Kuma shi wannan fim ɗin nawa na farko kusan duk waɗanda ke cikinsa sun koma ga Allah.

Mafi yawan finafinanki a uwa kike fitowa. Me ya sa kika fi son fito wa a wannan matsayin?

(Dariya) A’a, ba ni ce na fi so ba, fim ne kawai, su waɗanda suke ba ni irin wannan matsayin wata ƙila suna samun abinda suke so ne, duk da yake ana ɗan caccanza min, amma da yake wancan ya fi yawa shiyasa ya danne duk wani wanda zanyi, saboda na fi fito wa uwar jarumi ko jaruma, amma an fi ba ni mahaifiyar ya’ya maza, kuma galibi iyaye maza sun mutu sai ni da ‘ya’yana gidan masu kuɗi ko mara sa kuɗi, amma ba ni na ke zaɓa ba.

Daga lokacin da kika fara fim zuwa yanzu kin san adadin finafinan da kika yi?

Eh to, a gaskiya shekara shida kenan na daina lissafi, amma a ƙiyasce na yi finafinai fiye da 350, daga cikinsu akwai: ‘Kudura’, ‘Ba’asi’, ‘Qara’i’, ‘Ibro Ɗan Zamani’, ‘Gidan Biki’, ‘Wani Gari’, ‘Tsuntuwa’, ‘Giwar Ƙarfe’, ‘Marainiya’, ‘Gidan Kitso’, ‘Maraici’, ‘Mahaifiyarmu’, da kuma ‘Attajira’.

Ko za ki gaya mana wata fitowa da idan kika tuna ta kike jin daɗi?

Gaskiya na yi su da yawa, amma duk da haka bayan dawowata fim 2012 akwai wani fim ‘Ƙara’i’ shi ne bazan iya mantawa da shi ba, saboda fim ne da ya zo da sabon salo kuma a lokacin an yayata shi kuma anan ne duk wanda ya ganni sai ai ta maganganu akan ashe na dawo fim.

Sai kuma fim ɗin ‘Wani Gari’ shi ma bazan manta da shi ba, na ji daɗin sa, domin an bani ‘Script’ wata biyu kafin a fara ɗaukar fim ɗin, don haka sai da ya zama na haddace gabaɗaya labarin, kuma fim ɗin shi ne ya tada min da tsimin son fim, kuma da shi ne harkar fim ta ƙara shiga raina kuma ta gogar da ni.

Waɗanne irin nasarori kika samu a masana’atar Kannywood?

Alhamdulillahi! Na samu nasarori da yawa a harkar fim, alfarma da ake yi mana sanadin fuskarmu ita ma nasara ce, yanzu haka yarinta tana ‘School of Hygiene’ gabaɗaya al’amarin makarantarta alfarmar fim ce, kuma akwai ‘yan fim da yawa waɗanda ni ce silar shigowarsu Kannywood, yanzu haka a wannan ‘location’ ɗin akwai yaron da sanadiyyata an sanya shi a wannan fim, kuma wuri mai kyau, wasu ma sai mun haɗu sai su same ni su ce ai su ne waɗanda na yi magana aka sanya su a fim.

Kuma akwai kamfanoni kamar Khairiyya Fim Production da kamfanin Ali Rabi’u Ali Daddy da GSharif25 sun ba ni matsayin uwa da na ke zama da yara mu na ba su horo na musamman akan fim. Don haka babu abinda za mu cewa Allah sai godiya.

Waɗanne irin ƙalubale kike fuskanta kawo yanzu a wannan masana’anta?

Ƙalubale musamman a wannan ƙasa ta mu ta Kano, wato ka san ƙasa ce ta malamai da al’umma daban-dadan, to har yau za ka ga fim bai shiga jikin jama’a ba, sai ka ga wani yana yi maka wani kallon don kawai kana fim, wani lokacin har raina ya kan ɓaci, mu ma ‘ya’ya ne, mu ma masu usuli ne, ba daga sama aka jefo mu ba, kuma ba daga wata uwa duniya aka jefo mu ba, kuma duk bawa ba zai wuce ƙaddararsa ba, don haka idan akwai ƙalubale ba zai wuce wannan ba.

Wasu na cewa, masana’atar Kannywood wuri ne na sheƙe aya da rashin tarbiyya musamman mata. Me za ki ce akan haka?

A cikin kowacce mu’amala ta rayuwa akwai mai kyau akwai mara kyau, kuma kowanne tsuntsu kukun gidansu yake yi, idan ka ga mutum ba shi da tarbiyya a cikinmu to dama haka ya zo da kayansa ya zo.

Kuma ɗan tarbiyya duk inda ya shiga, ba zai cire rigar gidansu ya jefar ba, saboda haka ba fim ba ne. Da kafin fim yan zaman shahada na Saudiyyya ne su ake ɗora wa balai’n duniya, ‘yar zaman Shahada ko a Ka’aba ta ke kwana ‘yar iska ce, yanzu kuwa fim ya karɓe wannan.

Wane ne ubangidanki a masana’atar Kannywood?

Ba da alfahari ba, ni gaskiya ba ni da wani ubangida, da kafata na shigo harkar fim, kamar yadda na gaya maka ni mace ce mai karance-karance don haka ni jagorata a harkar Hausa fim Mujallar Fim ce, domin na sayi Mujallar Fim Sulai bakwai a Bata, haka na ke sayo ta, Ina karantawa.

To, da na samu wani ɗan bacin rai a rayuwata ta aure to kawai sai na ce ni fim zan yi, har wata yar’uwata ta ke cewa, ah gaskiya za ta nema min tsari akan Allah ya kiyaye ya tsare ni da shiga fim, na ce saboda me za ki ce haka? Su waɗanda suke yi ba ‘ya’ya ba ne? Ai su ma ‘ya’ya ne haifarsu akai.

To haka dai kamar da bakin mala’iku ga shi da rabon zan yi ɗin. Don haka ni babban ubangidana bai wuce Mujallar Fim ba, domin da ita na samu addireshoshi na kamfanonin fim.

Duk da yake na je kamfanoni daban-dadan mun zauna da su, amma ban fara fim ba sai ta hannun marigayi Tjjini Ibrahim, don ya sanya ni a fim din ‘Ƙudura’, to ka ga idan Ina da wani ubangida ba zai wuce Marigayi Tijjani Ibrahim ba, haka na ke aikina a masana’atar, amma a ce ko a mutu ko a yi rai a ce wai wane ne ubangidana, wanda duk wani abu idan ya taso ya sa a nemoni gaskiyar magana ba ni da shi.

Menene fatanki na ƙarshe ga masoya da abokan aiki na Kannywood?

Mu na yi masu fatan alheri. Allah ya bar ƙauna. Abokan aiki kuwa Ina yi masu fatan samun nasara da fatan Allah ya ƙara ƙwarin gwiwa.

Mun gode.

Ni ma na gode ƙwarai.