Yadda aka kama wasu ma’aikatan banki da laifin satar miliyoyin naira a asusun mamaci

Jami’an Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Ƙasa Zagon Ƙasa, EFCC, reshen Makurdi sun kama wasu ma’aikatan banki bisa zargin satar Naira 4,199,500 mallakin wani kwastoma da ya mutu.

An kama waɗanda ake zargi, Idah Ogoh da Agbo Okwute, a ranar Jumma’a, 21 ga Yuni, 2024 a garin Makurdi, Jihar Benuwai.

Cafke su ya biyo bayan ƙorafin da bankin ya shigar a kansu bisa zargin cirar kuɗi daga asusun marigayin, Emmanuel Azer Agenna ba tare da izini ba.

An gano wannan ɓarnar ne lokacin da iyalan marigayin suka je bankin domin neman ragowar kuɗin da ke cikin asusu.

Iyalan sun nuna rashin amincewa da adadin kuɗin da bankin ya basu sannan suka aika da ƙorafi ga bankin game da cirar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba a asusun mamacin.

Sakamakon wannan ƙorafi, bankin ya gudanar da bincike na cikin gida, inda sakamakon ya bayyana cewa Ifah Ogoh, wanda ma’aikacin bankin ne, ya nema wa mamacin katin cire kuɗi a ranar 10 ga Mayu, 2023 kuma bankin ya amince buƙatar.

Sakamakon bincike ya kuma nuna cewa Ogoh ya yi amfani da katin da kansa wajen cire kuɗin bayan haɗa baki da Agbo Okwute wanda shi ma ma’aikacin bankin ne wajen sace kuɗin.

Ana kuma zargin cewa, daga baya an cire kuɗaɗen ta hanyar hada baki da Agbo a lokuta daban-daban duk dai ba bisa ƙa’ida ba.

Za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.