Yadda Shettima, Kwankwaso da Amaechi za su sauya alƙiblar zaɓen 2027

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Bayan manyan jam’iyyun siyasa sun bayyana sunayen waɗanda za su yi musu takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027, hankalin masu bibiyar siyasa ya karkata kan irin tasirin da waɗannan zaɓaɓɓun abokan takara za su iya yi wajen ƙara wa jam’iyyunsu ƙarfi a akwatin zaɓe.

Da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta rufe karɓar sunayen ’yan takara, shugaban ƙasa mai ci, Bola Ahmed Tinubu na Jam’iyyar APC zai sake neman wa’adin mulki tare da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima.

A ɓangaren Jam’iyyar ADC kuwa, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya zaɓi tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, a matsayin abokin takararsa.

Haka kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya zaɓi tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin mataimakinsa.

Fitowar waɗannan tikitin takara uku ta ƙara jawo hankali kan irin gogewar siyasa, karɓuwa a yankuna da kuma tasirin da mataimakan takarar ke da shi a tsakanin al’umma, wanda ake sa ran zai taka muhimmiyar rawa a yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na watan Fabrairun 2027.

A wajen APC, Kashim Shettima ya ci gaba da kasancewa mataimakin Tinubu bayan ya shafe shekaru yana wannan muƙami tun daga 2023. Tsohon gwamnan Jihar Borno kuma tsohon sanatan Borno ta Tsakiya ana sa ran zai taimaka wajen tabbatar da goyon bayan jam’iyyar a yankin Arewa maso Gabas.

Ana kallon yankin a matsayin ɗaya daga cikin wuraren da za a gwabza fafatawa sosai, musamman ganin cewa Atiku Abubakar ma ɗan asalin yankin ne kuma yana ƙoƙarin ƙarfafa tubalinsa na siyasa.

A zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Atiku ya lashe jihohin Adamawa, Bauchi, Gombe, Taraba da Yobe, yayin da Tinubu ya yi nasara ne kawai a Jihar Borno.

A tikitin ADC kuwa, zaɓen Amaechi ya kasance abin da masu nazari ke ganin zai taimaka wa jam’iyyar wajen ƙarfafa tasirinta a Kudu maso Kudu tare da faɗaɗa karɓuwarta a Kudu maso Gabas.

Amaechi, wanda ya taɓa zama Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ribas, gwamna na wa’adi biyu da kuma tsohon Ministan Sufuri, ya shafe shekaru masu yawa yana riƙe manyan muƙaman gwamnati da siyasa.

Shi ma yana cikin fitattun ’yan takarar neman tikitin shugaban ƙasa na APC kafin zaɓen 2023, inda ya zo a bayan Tinubu.

Ko da yake Tinubu ne ya lashe Jihar Ribas a zaɓen 2023, Peter Obi ne ya mamaye yawancin jihohin Kudu maso Gabas, sannan ya samu gagarumin goyon baya a wasu sassan Kudu maso Kudu.

A zaɓen fidda gwani na APC na 2023, Tinubu ya samu ƙuri’u 1,271, yayin da Amaechi ya samu 316, sannan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya samu ƙuri’u 235.

A ɓangaren NDC kuwa, ana ganin zaɓen Kwankwaso zai ƙara wa jam’iyyar ƙarfi a Arewacin Nijeriya, musamman a Kano da wasu jihohin Arewa maso Yamma.

Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano kuma tsohon sanata, ya shahara wajen kafa ƙungiyar Kwankwasiyya, wadda ake kallon tana daga cikin ƙungiyoyin siyasa masu ƙarfi a matakin al’umma.

A zaɓen 2023, ya lashe Jihar Kano cikin gagarumar rinjaye a matsayin ɗan takarar Jam’iyyar NNPP, inda ya kayar da ’yan takarar APC, PDP da Labour Party.

Ya samu kashi 58.4 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, inda ya kayar da Atiku Abubakar na PDP da tazarar kusan ƙuri’u 440,000. Tinubu da Peter Obi sun zo a baya da kashi 7.3 da kuma 1.8 cikin 100 bi da bi.

Sai dai fitowar Kwankwaso a matsayin mataimakin Obi ta zo ne bayan rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye tafiyar Kwankwasiyya, sakamakon saɓanin da ya shiga tsakaninsa da tsohon yaronsa na siyasa, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ya koma APC.

Masanin manufofin gwamnati da harkokin siyasa, Suleiman Hassan Gimba, ya ce bai kamata ’yan Nijeriya su ɗauka cewa mutum zai yi nasara a zaɓe saboda kawai waɗanda ke kan tikitin takara ba.

A cewarsa, abubuwa da dama ne ke tantance sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, ciki har da yadda jama’a ke kallon shugabanci, tsarin yaƙin neman zaɓe, kuɗaɗen gudanar da kamfen, tsaro, sahihancin zaɓe da kuma yawan masu fitowa kaɗa ƙuri’a.

Ya ce APC, ADC da NDC duk sun zaɓi mutane masu ɗimbin gogewar siyasa, amma hakan kaɗai ba zai tabbatar da samun ƙuri’u ba.

“Yanzu abin da ake jira shi ne kowace jam’iyya ta gamsar da ’yan Nijeriya cewa tana da mafita mai inganci kan matsalolin tattalin arziki da tsaro,” inji shi.

Gimba ya ƙara da cewa mataimakan takarar shugaban ƙasa kan kawo tsarin siyasa, dabaru da tasirin yankuna ga kamfen, amma bai dace a ɗauka cewa mutum ɗaya zai iya kawo wa jam’iyya nasara a jiha ko shiyya gaba ɗaya ba.

Ya bayyana cewa Kwankwaso na da ɗaya daga cikin ƙungiyoyin siyasa mafi ƙarfi a matakin ƙasa, Shettima kuma na da gogewa da fahimtar yanayin Arewa maso Gabas, yayin da Amaechi ke da ƙwarewar gudanar da gwamnati da tsara harkokin siyasa.

Shi ma malami a Sashen Kimiyyar Siyasa na Jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke Awka, Dakta Christian Okeke, ya bayyana Kwankwaso a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa da ya fi kowa ƙarfin mabiyan siyasa kai tsaye.

A cewarsa, ƙungiyar Kwankwasiyya ta tabbatar da ƙarfinta a zaɓuɓɓuka da dama, kuma ita ce babbar kadarar siyasar Kwankwaso.

Ya ce, duk da cewa Shettima na cin gajiyar kasancewa a kan mulki, Amaechi kuma na da ƙwarewar shugabanci, nasarar kowace jam’iyya za ta ta’allaka ne da yadda za ta iya jawo hankalin masu kaɗa ƙuri’a tare da gabatar da mafita ga matsalolin da suka fi damun ’yan Nijeriya.

Wasu tsoffin ’yan siyasa biyu, Peter Fakolujo da Isaac Kekefun, sun kuma yi nuni da cewa yanayin siyasa ya sauya sosai tun bayan da Amaechi ya nemi tikitin APC da kuma lokacin da Obi ya tsaya takara a ƙarƙashin Labour Party a 2023.

Fakolujo ya ce ba zai kasance abu mai sauƙi ba Amaechi ya kwace tasirin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, a Jihar Ribas, kasancewar dukkansu sun taɓa mulkin jihar.

A cewarsa, Wike na da tasiri a cikin PDP da APC a jihar, kuma yana da rinjaye a Majalisar Dokokin Ribas, lamarin da zai sa Amaechi ya yi aiki tuƙuru idan yana son samar wa Atiku ƙuri’u.

Sai dai ya ce Amaechi na iya anfani da fushin wasu ’yan APC da PDP da ba su gamsu da yadda aka tafiyar da al’amuran tsohon gwamna Siminalayi Fubara ba.

Ya kuma yi nuni da cewa a yanzu APC ce ke mulkin dukkan jihohi shida na yankin Kudu maso Kudu, wato Akwa Ibom, Bayelsa, Cross Riɓer, Delta, Edo da Ribas, wanda zai iya amfani wa jam’iyyar.

Isaac Kekefun ma ya amince da wannan ra’ayi, amma ya ce Amaechi mutum ne mai kuzari da ƙwarewa, wanda zai iya ƙara wa tikitin Atiku ƙarfi.

Haka kuma ya bayyana cewa zaɓen Kwankwaso a matsayin mataimakin Obi dabara ce mai kyau, domin yana iya taimaka masa samun ƙuri’u daga jihohin Arewa maso Yamma, musamman ganin irin farin jinin da yake da shi a Kano da tsakanin matasa da Musulman Arewa. A cewarsa, hakan na iya ƙara wa Obi karɓuwa a yankin Arewa.

A gefe guda kuma, wasu masu sharhi sun ce ci gaba da riƙe Shettima a matsayin mataimakin Tinubu ya taimaka wajen daƙile sabuwar muhawara kan sauya tikitin APC.

Malam Abubakar Dahiru ya ce cire Shettima domin maye gurbinsa da Kirista, kamar yadda wasu suka taɓa nema, zai iya haddasa sabon rikici a cikin jam’iyyar.

Ya ce yanzu muhawarar tikitin APC ta ƙare, abin da ya rage shi ne gwamnati ta mayar da hankali kan tattalin arziki da tsaro. Ya kuma bayyana cewa al’ummar Borno da Kanuri da dama sun yi maraba da ci gaba da kasancewar Shettima a tikitin APC, yayin da gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umara Zulum, da wasu gwamnoni daga Arewa suka taya shi murna.

Sai dai Dahiru ya ce Shettima zai yi ƙoƙari sosai wajen jan hankalin masu kaɗa ƙuri’a a Arewa maso Gabas, domin yankin gida ne na Atiku Abubakar.

By ukarofi

Leave a Reply