Yadda ‘yan siyasar Nijeriya suke “halatta wa” kansu dukiyar ƙasa

Daga MUHAMMAD SULAIMAN ABDULLAHI (Phd)

Dukiyar Nijeriya za ta daɗe ba ta amfanar da talakawanta ba, musamman idan aka tafi a kan wannan jirkitaccen tsarin na kashin dankali. Tuni da yawa daga cikin ‘yan siyasa da manyan ma’aikatan gwamnati har ma da wasu ƙananan, da kuma wasu marasa kan gado daga cikin talakawa suka halatta wa kansu irin wannan dukiya ta qasa ba tare da jin wani ɗar ba. Ci kawai suke yi ba ƙaƙƙautawa, kuma “halal” suke ci, mafi ƙaranci ka ce a tunaninsu. Ina da dalilai da yawa kamar yadda zan bayyana a wannan rubutu.

Bari in fara abin daki-daki. Kuma zan fi mayar da hankali a kan kaso uku na ‘yan Najeriya, waɗanda a ganina su ne suka fi zaluntar kowa game da dukiyar ƙasa, kuma ta hanyar halattawa kai! Ga su kamar haka:

1) ‘Yan siyasa
2) Manyan ma’aikatan gwamnati
3) Talakawa

A duk inda na ambaci wasu rukunin jama’a, to ina magana ce a kan wasu daga cikinsu, ko mafiya yawa. Domin ni kaina na san ba duka aka taru aka zama ɗaya ba.

1) Rukuni na farko – ‘Yan siyasa:

‘Yan siyasa su ne suka fi kowa “halatta wa” kansu dukiyar Najeriya. Kuma fa su, yawancinsu, musamman ma masu tsoron Allah a cikinsu, a wajensu halal suke ci, domin kawai haka ƙasar ta tsara musu, kuma sun amince cewa ba za su iya gyarawa ba.

E! Na yi magana a kan masu tsoron Allah, kuma zan yi ƙarin bayani. Misali, akwai wani wa’azin Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami – Allah Ya qara masa lafiya da tsoron Allah, – a wa’azin, yake bayyana cewa wani ɗan siyasa ya ga wasu mazajen kuɗaɗe a cikin asusun bankinsa. Sai shi ɗan siyasar ya tambayi abokan aikinsa, ya ce nasu ne su duka ‘yan majalisa amma aka turo masa shi kaɗai? Mai ba shi amsar, wani ɗan’uwansa ɗan majalisa ko minista (na manta) ya bayyana masa da cewa nasa ne shi kaɗai. Ɗan siyasar nan, da yake sabon shiga ne, kamar yadda Malam ya bayyana, sai ya tambaya, ya ce, “anya kuwa za mu ga Annabi, in muna aikata irin wannan?” Sai abokin aikin nasa ya bayyana masa cewa “ai in Annabi kake so ka gani, bai kamata ma ka zo nan ba”! Wannan labari Sheikh Pantami ne ya bayar da shi, duk mai son jin cikakken labarin, zai iya bincikawa a YouTube.

Wani abin izina daga wannan labari, waɗannan fa da Malam ya bayar da labarinsu duk Musulmi ne, waɗanda suke fatan su tashi a tutar Annabi Muhammadu (S.A.W), a ranar alqiyama, to ina kuma ga sauran gama garin ‘yan tasha da muke turawa kawai saboda muna ganin suna da kuɗi ko kuma kawai saboda sun ba mu kuɗi?

Ko da shi Malam Pantami, akwai wani abu da ya tava faɗa, bayan ya hau mulki. Duk da har yau ina ganin qimar Malam, kuma ina yi masa addu’a kuma zan cigaba da yin hakan, amma a gaskiya sai da na yi mamakin abin da ya faru! A wani taro ne, shi Malam Pantami da kansa, ina jin a lokacin ya zama minista, ko kuma yana NITDA ne, yake bayyana cewa gwamnan Borno, Farfesa Umara Zulum, ya ba shi kyautar wasu kayan sawa har kusan guda 40! Duk da za a ga wannan kamar ba komai ba, to amma meye matsayin ba wa ma’aikacin ofis irin wannan kyautar a musulunce a lokutan da yake kan gudanar da ayyukansa? Ba wai bayan ya sauka ba ko kafin ya hau? Na san dai a dimokuraɗiyyance wataqila ba komai, amma dai gaskiya a addinance kamar akwai matsala.

Haka kuma, akwai wani ɗan siyasa mai imani, kuma mai mutunci, yana da alaƙa da addini sosai, amma wani labari ya zo min cewa ya kafa jami’a saboda son al’ummar yankinsa, a wata jiha, amma bayan an kammala ginin jami’ar, an kashe maƙudan miliyoyin nairori (sai ka yi mamakin ta ina ya samo waɗannan maƙudan kuɗin, alhalin kowa ya san kafin ya fara siyasa ba shi da su) sai aka yi wani zama ana so a fara ayyukan jami’ar!

An ce a wajen zaman wasu masana suke ba shi shawarar cewa in ana so jami’ar ta fara aiki yadda ya kamata, tun daga sayo kayayyakin aiki, da ɗaukar ma’aikata da sayen kayan gwaje-gwaje da ruwa da wuta da albashin ma’aikata, da tallace-tallace da buge-bugen takardu da sauran abubuwa irin waɗannan, to ana ganin sai ya tanadi kusan Naira biliyan uku! Biliyan uku fa! Wannan fa yana nufin Naira Miliyan Dubu Uku fa! Kuma wannan ba fa a maganar abin da ya kashe a aikin gine-gine da neman lasisi da sayen filin wajen da sauransu. Kuma fa shi wannan mai imani ne in aka kwatanta shi da ragowar. To tambayar ita ce, ta wace hanya ya samo waɗannan maƙudan kuɗaɗen? Ko ya samo kuɗin da aka ba shi shawarar, ko bai samo ba, ko bashi ya ciwo, Allah ne masani!

A irin wannan dai, wani abokin wani ɗan majalisa yake ba ni labarin yadda shi wannan ɗan majalisar ya sami alawus na Naira miliyan ɗari takwas a sakamakon zaman wani kwamiti da shi ɗan majalisar ya shugabanta. Mai karatu ya kamata fa ka gane, ba wai cewa aka yi ya sata ba fa! A’a sam! “haƙƙinsa” ne na “halal” da gwamnatin Nijeriya ta ba shi a sakamakon wannan zaman na kwamiti da aka ce an yi!

Hakan za ka gani, yadda wasu daga cikin ma’aikatan gwamnati, waɗanda muke kyautatawa zaton alheri, amma sai ka ga suna ta facaka da kuɗi, ka ji mutum shi ba ɗan kasuwa ba, babansa ba ɗangote ba ne, kuma albashinsa na halal da aka sani bai fi miliyan ɗaya ba, amma sai ka ji ya ba da kyautar Naira miliyan ɗari. Wannan fa kusan albashinsa na shekaru goma kenan, amma kuma shi, bai ma yi shekaru biyar a kan kujerar ba. Ko ka ga mutum ya yi ginin sama da Naira miliyan ɗari a wani waje.

Ko ka ji ya bayar da kyautar injinan markaɗe ko kekunan ɗinki ko mashinan hawa na miliyoyin kuɗi, yana rabawa, mu kuma muna karɓewa muna murna muna dariya, muna cewa Allah ya kare su! Waɗannan fa masu imanin cikinsu kenan, waɗanda ma suke iya tunawa da talaka, wani lokaci a yayin buƙatar sake ɗarewa kan kujerar mulki, ko kuma a yayin wata buqata ta ƙashin kai!

Yanzu ku dubi yadda gwamnatin Buhari take wadaƙa da dukiyar al’umma, ta fuskar tafiye-tafiye na babu gaira babu dalili, da shiga jirage da hawa motoci… har bikin haihuwar ‘yar shugaban ƙasa aka yi a ƙasar Turkiyya. Ba kunya ba tsoron Allah! Kuma wai kuna zaton da kuxin aljihunansu na ƙashin kansu suke wannan facakar? In kuɗin aljihunansu ne, me ya sa ba su yi kafin 2015 ba?

Kalli yadda suke kashe kuɗin al’umma a bukukuwansu mana. Wannan fa ba a maganar rigunan sawa na miliyoyin nairori da agoguna da motoci, kai hatta masai, masai ta yin kashi ta gidan shugaban qasa, in ka ji irin kuɗaɗen “halaliya” da aka halatta mata, za ka sha mamaki. Kuma fa duk waxannan kuɗin na “halal” ne, amma fa halal wadda masu mulki, musamman ‘yan siyasa suka halattawa kansu.

In ba haka ba, ta ina za ka ga wani ɗan siyasa ya sami sama da albashinsa a siyasa? Kuma maƙudan kuɗin da suka haura hankali! Da yawa fa daga cikin kuɗaɗen nan, har a labarai ma ana faɗa. Allah ne kaɗai ya san miliyan nawa kunnen shugaban ƙasa ya ci, a lokacin da aka ce yana ciwon kunne, kuma ya tafi Ingila don a duba kunnensa. Da wahala in da kuɗin aljihunsa ya tafi, tun da za ka ga akwai wata hanya ta halaliya da ‘yan siyasa suka samar wa kansu da shugaban ƙasa da ma waɗanda ba su kai shi ba, da za su iya fita waje a duba lafiyarsu, ta “halattacciyar” hanyar da suka halattawa kawunansu.

Galibin ‘ya’yansu da suke karatu a waje, ba da kuɗin aljihunsu suke kai su ba. Suna kai su ne a ƙarƙashin “scholarships” na hukumomin gwamnati, saboda sun halattawa kansu waɗannan hanyoyin, alhali ga asibitocin talakawa nan birjik suna cikin matsananciyar masifar rashin komai. Ga jami’o’i nan a rufe, amma masu imani a cikinsu, suna can suna cin “halal” ɗinsu ba ƙaƙƙautawa.

2) Rukuni na biyu – Manyan ma’aikatan gwamnati:

Su kuwa waɗannan, musamman manyan cikinsu, idan aka yi rashin sa’a, su suke koyawa masu mutunci da ma marasa mutunci daga ‘yan siyasa, hanyoyin da za su bi su yi zalunci. Yawanci da su da ‘yan siyasa tare suke haɗe kai su turmushe talaka. Ka ga mutum ya daɗe yana zaluntar al’umma a kan wata kujerar aiki, amma a duk shekara zai bayar da sadakar kunu da azumi ko ya biya wa wasu kujerar Umara, amma wataƙila da hannunsa a wajen wahalar man fetur, ko cuwa-cuwa a ofishin kwastan ko ofishin ‘yan sanda ko ofishin imigireshan ko a wajen yin paspot ko a wajen samar da wuta ko ruwa ko ilimi ko tituna ko tsaro ko harkar noma ko lafiya ko sarauta ko ɓangaren Shari’a… ko ma dai dukkanin ofisoshin ƙasar nan. Kusan a kowane ofis, sai ka sami wani babban mugu da ya halattawa kansa haram, ko kuma yake ma cin haram ɗin ƙiri-ƙiri ba tare da wani shayin kowa ba! A irin waɗannan “halattattun” hanyoyin, Allah ne kaɗai ya san adadin Tiriliyoyin dalolin da suka zurare, kuma aka saka al’umma cikin halin ƙunci da masifa.

3) Rukuni na uku – Sauran talakawa:

Su kuwa sauran talakawa, nasu “halattattun” hanyoyin kaɗan ne, amma in aka tattara su, sai sun kusan kai wa na wasu ƙananan manyan azzaluman. Kwanan nan, akwai wani bidiyo na wani yaro da aka dinga yaɗawa, wanda aka kama shi ya ɓamɓare ƙyauren wani ƙofar wani Police Station ya sace, ko wani abu makamancin haka. Yaron da aka yi hira da shi, Salisu Zango na Freedom Rediyo ne ya kawo rahoton, bayan an kama yaron, bai ma yi nadama ba, kuma ya bayyana cewa duk wata kadarar gwamnati ganima ce a wajensu. Ya ce ko wata motar ‘yan sanda ce ta paka a wani waje, za su iya cire taya ko batir, domin dukiyar gwamnati ce don haka “halal” ce a wajensu.

Irin waɗannan suke iya ɓalle ƙarfunan jikin katangun hukumomin gwamnati su sayar – ka duba jikin jami’ar NorthWest da ke Kano, duk irinsu-irinsu sun bi su ɓaɓɓalle ƙarafunan jikin katangar sun ƙwaƙule sun sayar. Su ne suke jijjige ƙarafan titin jirgi su sayar. Su ne suke ƙirƙirar matatun man fetur, su ma duk “halal” ne s wajensu, tun da sun san akwai wasu waɗanda su ma sun halattawa kansu dukiyar ƙasa. To don me su ba za su yi ba?

To mutum nawa ne a Nijeriya a yau, za su farka su ji an antayo musu wasu hamshaqan kuɗaɗe daga wuraren ayyukansu, amma su tsaya tambayar na meye? Mutum nawa ne za su tambayi dalili? Don haka, abu ne sananne, gwamna zai iya busar iska, ya tura wa ‘yan majalisa, Naira miliyan-miliyan, kowannensu, musamman idan yana so ya zaftaro wasu biliyoyi shi ma ya “halattawa” kansa, amma a cikin ‘yan majalisar, waye zai tambayi na me ye? Da wahala ka sami ko ɗaya, har limaman cikinsu.

Daga cikin talakawan da suke halattawa kansu dukiyar ƙasa, akwai wasu daga cikin malamai da yaran ‘yan siyasa, waɗanda ake ba su maƙudan daloli, amma ba za su tambayi don me ba, kuma ba za su tambayi daga ina aka samo su ba. To gara ma su, ai ba su aka yi. Amma duk da haka, yawaitar hakan ba ƙaramin zalunci ba ne ga ƙasa, musamman ma in har masu karvar suna da masaniyar zaluncin masu bayarwar!

Haka ‘yan kasuwar da suke iya yin takardun bogi, kawai don su cimma manufarsu ta samun ƙashin miya. Su ma sun halattawa kansu irin waɗannan hanyoyi don sun san shugabanninsu ma suna yin hakan.

Ko yadda Buhari yake tafiyar da gwamnatin Nijeriya a yau, kamar yadda na faɗa a baya, cikakkiyar amsa ce ta yadda shugabannin siyasa da miyagun ma’aikata gwamnati suke halattawa kansu dukiyar ƙasa.

Za ka fahimci wannan idan ka ji cewa matar shugaban ƙasar Amurka, Michel Obama, ta tava bayyana cewa ko gyaɗa suka ci a White House, to fa sai sun biya. Kai yanzu akwai wanda ya isa ya sa Buhari ya biya kuɗin abincin da ya ci da iyalansa a Villa? Ai ba shugaban ƙasa ba ma, abokin ƙanin mai yankan farcen shugaban kasa ma, in dai yana da hanyar shiga Villa, to a kyauta zai dinga shan romon dimukuraɗiyyar dalolin Najeriya, ba tare da wata wahala ba.

Yo in ba haka ba, ta ina mawaƙin jam’iyya zai yi mahaukatan kuɗin da zai iya hawa jirgin shugaban ƙasa, zai iya bayar da kyautar motoci ɗari, zai iya sayan gidan sama da miliyan ɗari… zai iya duk abin da ya ga dama? To a haka ma fa, har gara mawaƙi ma. Shi yana ma da fasaha. Amma wani ma za ka samu ƙungurmin daƙiƙi ne, amma an halatta masa dukiyar qasa ta wata hanya yana abin da ya ga dama da ita.

Don haka dai jama’a, da yawa daga cikin mahukuntan Nijeriya “halaliyarsu” fa suke ci, a tunaninsu, domin sun daɗe da halattawa kansu irin waɗannan mugayen miliyoyin nairori, kuma a wajensu, kai ne ma gaula ba ka gane ba!

Mafita, ka zavi wanda kake da tabbacin ba zai yi haka ba. Ko kuma in ya tashi halattawa kansa, zai halattawa kansa kaɗan. Ai da babban mugu, gara ƙarami! Akwai wanda za ka samu, ɗan majalisa, ko wani shugaba daban, shi kaɗai, ya fi dukkanin jama’ar da suka zaɓe shi cin kuɗin kujerar da aka zaɓe shi don yi wa al’umma aiki. Misali, in an sami miliyan goma ta hanyar ofishinsa, za ka ga shi kaɗai ya cinye miliyan tara da rabi! To irin waɗannan, me ye amfanin su?

Allah Ya ba mu shugabanni masu hankali da imani da tsantseni da sanin ya kamata, amin!

Muhammad Sulaiman Abdullahi. Ɗan ƙasa ne mai bayyana ra’ayi. Ya rubuto daga Jami’ar Bayero, Kano.