‘Yan bindiga sun sace shugaban ƙaramar hukuma a Nasarawa

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga yankin Karamar Hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa sun ce, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban hukumar, Mr. Safiyanu Isa Andaha.

Hadimin Gwamnan jihar kan lamurran kananan hukumomi da masarsutu, Haruna Kassimu ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an sace Safiyanu Isa ne a kauyen Ningo da ke hanyar Akwanga – Andaha a yankin.

Ya kara da cewa, an sace shugaban karamar hukumar ne tare da wani mai suna Alhaji Adamu Tanko Custom da misalin karfe 8:30 na daren Litinin da ta gabata.

Kazalika, Kassimu ya ce jami’an tsaro sun dukufa bincike inda suka bi sawun ‘yan bindigar domin kwato wadanda aka yi garkuwa da su.

Haka shi ma mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya ce ‘yan sanda tare da hadin gwiwar takwarorinsu sun bi sawun barayin don tabbatar da an ceto wadanda lamarin ya shafa.

Ba wannan ne karon farko da irin haka ke faruwa a jihar ta Nasarawa ba, ko a lokutan baya ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban Karamar Hukumar Keffi,Hon Babab Shehu, inda daga bisani aka sako shi bayan an biya kudin fansa.