Zaɓen 2023: Ban bayyana ƙudirina na takarar shugaban ƙasa ba – Osinbajo

Daga FATUHU MUSTAPHA

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, ya ce shi dai bai bayyana ra’ayinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa ba a 2023. Yana mai cewa ɗaga wanna zance a yanzu neman karkatar da hankali ne kawai.

Sanarwa da mai magana da yawun Osinbajo, Laolu Akande ya fitar a Litinin da ta gabata, ta nuna ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ba shi da alaƙa da  wani gangamin goyon bayan tsayawa takara da aka shirya ta intanet.

Sanarwar ta ce, “Hankalin Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ya kai ga wani shafin intanet ‘supportosinbajo.ng’ wanda ke kira ga ‘yan Nijeriya da su zo a haɗa kai wajen mara wa Osinbajo baya yayin babban zaɓen 2023.

“Yanzu haka ana nan ana ci gaba da yaɗa bayanan wannan shafin da neman a shigo cikin tafiyar bisa cewa Osinbajo ya bayyana ra’ayinsa na tsayawa takara a 2023 a fakaice.

“Ofishin Mataimakin Shugaban Kasar ba shi da alaƙa da wannan shafi na intanet ko waɗanda suka shirya hakan ta kowace hanya, tare da bayyana haka a matsayin neman raba hankali.

“Osinbajo bai bayyana ra’ayinsa kan neman takarar shugaban ƙasa ba ya zuwa 2023, maimakon haka ya maida hankalinsa ne wajen yin aiki a matsayinsa  na nataimakin shugaban ƙasa a wannan gwamnati mai ce domin magance matsalolin ƙasa ciki har da ƙoƙarin lalubo mafita mai ɗorawa game da matsalolin tsaron da suka addabi ƙasa.

“Don haka muna kira ga jama’a da a guje ma aikata irin wannan al’amari wanda ba zai taimaka da komai ba sannan mu haɗa hannu mu fatattaki matsalolin da suka yi wa Nijeriya dabaibayi don amfanin kanmu da zaman lafiyarmu a cikin ƙasa.