Zabtare Ma’aikata: Ba gudu ba ja da baya, cewar El-Rufai

  • Sufeto Janar ya bada umarnin tura ƙarin dakaru zuwa Kaduna

Daga AISHA ASAS

Sakamakon zanga-zangar lumana da Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) reshen jihar Kaduna ta gudanar a Litinin da ta gabata da kuma soma yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyar, ya sa harkokin kasuwanci sun tsaya cak a jihar. NLC ta ɗauki wannan mataki ne domin ƙalubalantar korar ma’aikata su 4,000 da Gwamna Nasir el-Rufai ya yi kwanan nan.

Gwmna El-Rufai ya ce game da matakin rage yawan ma’aikata da ya ɗauka ba gudu ba ja da baya, tare da cewa matakin yajin aikin NLC ba zai sanya gwamnatin jihar fasa aikata abin da ta sa a gaba ba. Haka ma ita ma NLC ta ce ba za ta ja da baya dangane da matakin da ta ɗauka har sai gwamnatin jihar ta yi abin da ya kamace ta.

Biyo bayan matakin shiga yajin aikin da ma’aikata suka ɗauka a jihar Kaduna, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Usman Alkali Baba, ya bada umarnin a tura ƙarin dakaru da kuma kayan aiki ya zuwa juhar domin kare al’umma da kuma tabbatar da tsaro a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Mai Magana da Yawun ‘Yan Sanda na Ƙasa, CP Frank Mba, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Litinin a Abuja.

Ya ce Sufeto Janar ya bada umarnin haka ne domin tabbatar da kariya ga rayukan al’umma da na matafiya duba da yiwuwar samun cinkoson abubuwan hawa a babbar hanyar Kaduna sakamakon zanga-zangar ma’aikatan.

Kazalika, Babban Sufeton ya sake bada umarnin mataimakan babban sufeton da kwamishinonin ‘yan sanda na shiyya da na jiha da hurumin aikinsu ya shafi babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja da kewaye, da su tabbatar da ba a samu salwantar rayuka da dukiyoyin al’umma ba a yankin.

Mba ya ce Babban Sufeton ya bai wa al’umma tabbacin rundunarsu za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen sauke nauyin da ya rataya a kanta na bai wa al’umma kariya. Kana ya yi kira ga al’umma, musamman mazauna ƙauyuka da masu abubuwan hawa da masu zirga-zirgar kayayyaki a hanyar Kaduna zuwa Abuja, su bai wa jami’an tsaron da aka tura yankin haɗin kan da ya dace.

Haka nan, ya buƙaci jama’a su zama masu taimaka wa jami’an nasu da muhimman bayanai waɗanda za su taimaka wajen yaƙi da muggan laifuka a yankunansu.

Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa reshen Jihar Kaduna ta gudanar da zanga-zangar lumana ne domin nuna rashin jin daɗinta kan matakin zabtare ma’aikata da gwamnatin jihar ta yi, lamarin da ya haifar da ɗar-ɗar a jihar wanda ya ja hankalin rundunar ‘yan sanda zuwa ga tura ƙarin dakaru a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *