NFF ta taya Okala murnar cika shekara 70 da haihuwa

Daga FATUHU MUSTAPHA

Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta aika da saƙon taya murna ga tsohon mai tsaron ragar Nijeriya, Emmanuel Okala, wanda ya cika shekara 70 da haihuwa a ranar Litinin 17, Mayu, 2021.

Babban Sakataren NFF, Dr Mohammed Sanusi, ya yaba wa tsohon ɗan wasan bisa irin rawar da ya taka wa Nijeriya a fagen wasan ƙwallon ƙafa a matakin ƙasa da kuma a matakin ƙungiyar Rangers ta Enugu.

Ya ce, “Ba mu mance irin ƙoƙarin da Emmanuel Okala ya yi ba a zamaninsa inda ya yi wa Nijeriya hidima gwargwadon hali. Muna yi masa fatan alheri, fatan samun ƙarin lafiya mai inganci da kuma ƙarin shekaru masu albarka.

A zamaninsa, Okala ya yi ƙaurin suna a tsakanin takwarorinsa masu tsaron raga irin su Inua Rigogo, Peter Fregene, Amusa Adisa da kuma Eyo Essien.

Okala ya samu karramawarsa ta farko ne yayin wasan sada zumuntar da Nijeriya ta buga da Tanzania a Legas inda Nijeriya ta lallasa abokiyar karawarta da ci 3 da 2.

Haka nan, yana daga cikin tawagar ‘yan wasan Nijeriya da suka samu kyautar zinari yayin gasar Wasannin Motsa Jiki na Ɗaukacin Ƙasashen Afirka da aka yi a 1973 a Legas, tare da shi ne tawagar Nijeriya ta samu nasarar lashe gasar Cin Kofin Afirka a 1980, da dai sauransu.

Kazalika, Sanusi ya miƙa saƙon taya murna ga kyaftin ta Super Falcons, Asisat Oshoala, bisa nasarar da ƙungiyar da take buga wa wasa FC Barcelona, ta samu a kan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea da ke Ingila a gasar cin kofin UEFA ta mata.