APC ta musanta fitar da jadawalin babban taronta

Daga UMAR M. GOMBE

Jam’iyyar APC ta ce ba ta shirya gudanar da babban taronta ba kamar yadda ta ga wasu kafofin yaɗa labarai sun yaɗa.

Jam’iyyar ta ce rahoton taron nata da aka yaɗa shiryayyen al’amari ne wanda  aka tsara domin kitsa bahaguwar fahimta a cikin al’umma.

Sanarwar da ta fito daga hannun sakataren tsare-tsren babban taron jam’iyyar, John James Akpanudoedehe, ta nuna rahoton shiri ne kawai na masu neman ci da siyasa.

Sanarwar ta ce, “An ja hankalinmu kan wani shiryayyen labari da aka yi ta yaɗawa a wasu kafafen yaɗa labarai dangane da cewa APC ta shirya gudanar da babban taro na ƙasa har ta fitar da jadawalin tsare-tsarenta.

“Wannan ba komai ba ne face shiri na masu neman ci da siyasa waɗanda kan kewaya suna gabatar da kansu a matsayin ‘yan jarida wanda akwai buƙatar al’umma su guji irin waɗannan mutanen.

“Ba mu taɓa yin ƙarya ba game da ayyukan jam’iyyarmu kuma ba mu ga dalilin da zai sa mu aikata hakan ba. Salon jagorancin da Gwamna Mai Mala Buni yake yi a matsayinsa na shugaban jam’iyya na ƙasa ya ɗora APC a kan tafarkin gudanarwa mai inganci.

“Kwamitin riƙo na Jam’iyyar na aikinsa gaba gaɗi domin sauke nauyin da ya rataya a kansa wajen sake gina APC da daidaita mata zama tare da bai wa duka mambobinta kulawar da ta dace.”

Sanarwar ta ce a ranar Litinin, 17 ga Mayun 2021 Babbar Sakatariyar APC ta dawo bakin aiki bayan hutun bikin ƙaramar sallah da ta tafi don ci gaba da ayyukanta. Tare da cewa, za ta bayyana dukkan bayanan da jama’a ke da buƙatar sani game da harkokinta ta kafofin da suka dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *