Zaɓen 2023: Nijeriya ba za ta wargaje ba, inji Jonathan

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ya ce Nijeriya ba za ta wargaje ba sakamakon zaɓen 2023.

Jonathan ya bayyana haka ne a wajen taron Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afrika (ECOWAS) na majalisar masana da kuma tsare-tsare da aka gudanar a Legas.

Ya kuma bayyana ƙwarin gwiwarsa kan yadda ƙungiyar ECOWAS za ta iya magance ƙalubalen da ke fuskantar yankin.

A wani labarin kuma, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya ce tilas ne Nijeriya ta tunkari ƙalubalen yara fiye da miliyan 13 da ba sa zuwa makaranta a ƙasar nan, domin magance mummunar matsalar rashin tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Obasanjo ya bayyana haka ne ranar Litinin a Abuja a wajen taron shekara-shekara na gidauniyar Murtala Muhammed na bana.

Obasanjo, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Amintattu na Gidauniyar ta Murtala Muhammed, ya bayyana hakan ta hanyar wayar tarho, inda ya kuma jaddada cewa samun ɗimbin yaran da ba sa zuwa makaranta yana haifar da barazana ga tsaro a nan gaba.