Qatar 2022: An sauya ranar karawa tsakanin Nijeriya da Ghana

Daga WAKILINMU

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afrika ta sanar da takwararta ta Nijeriya cewa an sauya ranakun da tawagar Super Eagles za ta kara da Black Stars ta Ghana, a wasan neman gurbin zuwa gasar kofin duniya cikin watan Nuwamba.

Daraktan sadarwa na NFF, Ademola Olajire ne ya fitar da sanarwar, wadda ke cewa, “an sauya lokacin da za a buga wasannin share fagen zuwa gasar kofin duniya na Qatar 2022 tsakanin Nijeriya da Ghana.”

A baya an shirya cewa Super Eagles da Black Stars za su buga gida da waje a ranakun 24 da 27 ga watan Maris.

To amma yanzu za a fara buga wasan farko ne a filin Cape Coast na Ghana a ranar 25 ga watan na Maris, kafin a tafi filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja a ranar 29 ga watan na Maris.

Bayan kammala wasannin biyu za a san wanda ya samu gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar cikin watan Nuwamba.

Ƙasashen biyu sun daɗe ana damawa da su a fagen ƙwallon ƙafa a nahiyar Afrika, to sai dai tafiyarsu bata yi nisa ba a gasar cin kofin nahiyar ta AFCON da ba a jima da kammalawa ba a Kamaru.

Super Eagles ɗin dai sun kammala ne da Cape Verde da maki 13 a wasanni shida, kuma a ƙarshen wasannin share fage ne aka sallami tsohon kocin ƙungiyar Gernot Rohr daga muƙaminsa.

Ghana dai na buƙatar nasara ta ƙarshe a gida (1-0) da Afrika ta Kudu, domin ta zama ta ɗaya a rukunin G, da maki 13, ita ma Afrika ta Kudu ta zo ta ɗaya, domin ta fi Bafana ƙwallo ɗaya.

Black Stars kuma sun canja manajoji. An naɗa tsohon manajan Brighton and Hove Albion Chris Hughton a matsayin mai ba da shawara a fannin fasaha yayin da Otto Addo shine babban koci.

Nijeriya da Ghana sun haɗu sau 49 tun shekarar 1950 kuma Black Stars ce ke riƙe da kofin da ci 21 yayin da Super Eagles ta doke su 10.