Zaɓen mace ko namijin aure (II)

Assalam alaikum. Ina godiya ga Allah da ya sake ba ni damar rubuta wasiƙa zuwa ga ’yan uwana matasa a wannan jarida mai albarka ta Blueprint Manhaja.

Kamar dai yadda muka faɗa a makon da ya gabata cewa za mu cigaba da bada shawarwari ga matasa maza da mata kan zaɓar abokin/abokiyar zamantakewar aure. A yau za mu cigaba daga inda muka tsaya.

3- Rashin yalwa, talauci da tsadar aure: waɗannan suna daga cikin abin da kan kawo jinkirin aure ga samari, don haka bai kamata ba a bi al’ada da ƙuntatawa da tsanantawa ga kuɗin aure da za ta kai ga wannan jinkiri har ruhin samari da ’yan mata su gurɓata da ciwuka, ko miyagun halaye, sau da yawa jinkirin yana faruwa ne sakamakon:
a- Sanya sharuɗɗa masu wahala ga saurayi.
b- Yawan kuɗin da zai kashe kan kayan tanadin gida da sauransu.
A game da matsalar farko, al’umma ne ya kamata su sanya hannu wajen warwareta, amma matsala ta biyu al’umma da hukuma su ne zai zama sun sanya hannu wajen maganinta.

4- Ƙarancin amintuwa da juna tsakanin saurayi da budurwa, musamman akan samu wasu da yawan munana zato ga duk wanda suka haɗu da shi, ta yadda yakan yi musu wahala su yarda da shi, wanda kuma bai kamata hakan ya kasance ba.

Ta wani ɓangaren kuma wani lokaci jinkirin yakan taso ne saboda ruwan ido ko kuma tsanantawa wajen sharuɗɗan saurayi ko budurwa da za su aura wanda wannan ya kan ɗaukar musu tsawon lokaci ba su samu mai wannan sharuɗɗan ba, ko ma suka samun mai waɗannan sharuɗɗan. Mu sani binciken halin wanda za a aura saurayi ne ko budurwa yana da kyau, amma kada ya kai ga matsananci da zai fita daga al’adarsa.

Warware wannan matsalar yana hannun samari ne da ’yan mata?

Wasu daga matsalolin da saurayi ko budurwa kan iya fuskanta kafin aure ko bayan aure:

Wani lokaci saurayi da budurwa sukan fuskanci matsala ne kamar haka;

1- Burin da kowane ɓangare da iyayen saurayi da budurwa, ko su kansu saurayi da budurwa suke ci game da saurayi ko budurwa. Kamar kayan ɗaki da ya ke tunanin a kawo ta da shi da sauransu, ko kuma kayan lefe da ta ke tunanin ya kai gidansu don kada danginta su rai ta.

2- Nau’in sadakin da ake ayyanawa, ko kuma in ce kayan mun gani muna so da lefe a al’adunmu da ake sanyawa a kan saurayi, da idan suna da yawa yakan sanya jinkirin aurensa.

3- Kuɗaɗen kashewa domin bikin aure;

4- Tsanantawa wajen binciken laifuffukan juna;

5- Binciken matsayin dangin juna ta fuskacin wani muƙami ko dukiya.

6- Makahon so da zai rufe idanuwan juna da zai sanya kowanne ya kasa ganin laifin ɗayan domin a lokacin suna ƙishirwar juna, amma da zaran sun kawar da wannan ƙishirwar sha’awar sai a gane laifin juna: Daman burinsa shi ne ya san ta a matsayin ‘ya mace, shi kenan sai ya yi wurgi da ita.

7- Zargin juna da sukan yi ko son gaskiya ne ko na ƙarya tsakanin duka ɓangarorin biyu na saurayi da budurwa, ta yadda ɗayansu yakan ji tsoron ko son gaskiya ko na ƙarya ɗayan ya ke yi masa, ta yadda a nan gaba ɗayan su zai yi watse ya yi wurgi da abokin zamansa.

Sau da yawa mukan ga samari da ‘yan mata da yawa sun samu lalacewa sakamakon rashin yin aure da wuri, domin mutum idan ya balaga yakan zama kamar ɗanyar itaciya ce da idan ba a shayar da ita ba sai ta bushe. Wannan al’amari na halitta sau da yawa ya sanya wasu suka kasa kuma suka gajiya gaban sha’awarsu suka sallama ma ta, al’amarin da yakan janyo fasadi mai girma a cikin al’umma.

Daga cikin irin wannan fasadi zamu yi ƙoƙarin kawo misali da ɗaya ne daga ciki da ake cewa da shi istimna’i: Istimna’i wata mummunar ɗabi’a ce da takan samu samari ko ‘yan mata masu tashen balaga da su kan yi amfani da jikinsu ko hannunsu ko kayansu ko wani abu domin fitar da maniyyi daga gare su.

Za mu cigaba a mako na gaba, Insha Allah. Wassalam.

Daga Mustapha Musa Muhammad, ɗalibi a fannin karatun Injiniyancin Sinadarai (Chemical Engineering) a Jami’ar Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.