Za a fara cirar kuɗi da katin ɗan ƙasa a watan Agusta-NIMC

Daga Khadija Abubakar

Hukumar kula da katin zama ɗan ƙasa (NIMC), ta ce nan da watanni biyu za ta inganta katin zama ɗan ƙasa ta yadda zai ke amfani guda uku ga masu shi.

Wani jami’in hukumar da bai yadda a faɗi sunansa ba ya sanar manema labarai hakan a ranar Juma’a, inda ya ce kati zai fara amfani a matsayin shedar zama ɗan ƙasa, da ɓangaren cirar kuɗi kamar katin ‘ATM’ sannan da kuma wasu harkokin rayuwa.

Ya ƙara da cewa, hukumar tana iya ƙoƙarinta wajen cimma hakan, domin kuwa a halin yanzu, ta fara gwajin yiwuwar haka, dan haka take fatan kammala dukkan tsare-tsare a watan Agusta.

Daga, jami’in ya ce suna cigaba da tattaunawa da wakilan bankuna da sauran waɗanda lamarin ya shafa kan yiwuwar hakan da kuma ƙoƙarin don samar da adireshin yanar gizo ga tsarin domin cimma wannan kyakkyawan manufa ga ƴan Najeriya.