Za a jinginar da filayen jirgin saman Kano da Abuja

*Za a ƙara ciwo bashin Dala miliyan 800
*Za a nutsar da kuɗin a shirin rage raɗaɗin cire tallafin fetur

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Nijeriya ta amince a jinginar da filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da kuma Malam Aminu Kano da ke Kano.

Gwamnati ta amince da wannan mataki ne a taron majalisar koli da aka gudanar ranar Laraba a Abuja.

Ministan Sufirin Jiragen Sama a Nijeriya, Hadi Sirika, ya shaida wa BBC cewa za a jinginar da filin jirgin Abuja na shekara 20, sannan na Kano na tsawon shekara 30.

Sirika ya ce taron nasu ya kuma amince a sauyawa ma’aikatarsu suna daga ma’aikatar kula da sufirin jiragen sama zuwa ma’aikatar kula da sufirin jiragen sama da sararrin samaniya.

Ya kuma ce taron ya amince da wasu tsare-tsare da za su inganta harkokin sufirin jirage a Nijeriya.

Wannan ya zo daidai da lokacin da, Shugaba Muhammadu Buhari ke neman amincewar Majalisar Dattawa, domin karvo bashin Dala miliyan 800 daga Bankin Duniya.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar Dattawan ya karanta yayin zaman majalisar a ranar Talata.

Wasiƙar Shugaban Ƙasar ta yi bayanin cewa, za a ciyo bashin ne domin rage raɗaɗin da za a fuskanta bayan sanadiyar tallafin man fetur da za a cire.

Ana iya tuna cewa, wata sanarwa da Gwamnatin Tarayya ta fitar a watan Afrilu ta bayyana cewa, tallafin Dala miliyan 800 na Bankin Duniya za a yi amfani da shi ga ’yan Nijeriya masu rauni su miliyan 50 ko gidaje miliyan 10.

A cewar Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-Tsare, Zainab Ahmad, za a rarraba tallafin ne bisa shirin da aka yi na cire tallafin mai a watan Yunin bana.

Ministar ta ce ana ci gaba da aiki tare da sabon kwamitin miƙa mulki na Shugaban Ƙasa da gwamnati mai jiran gado domin tafiyar da shirin da ya hada da buƙatar samar da bas-bas da wasu buƙatu da dama.

Wannan yunƙuri na karɓo bashin na zuwa ne a daidai lokacin da Buhari ke shirin miƙa mulki a ranar 29 ga wannan wata na Mayu ga magajinsa, Bola Ahmed Tinubu da ya lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa a cikin watan Fabrairun da ya gabata.