An kashe Naira Biliyan 224 akan ƙidayar ƙasa da aka ɗage

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa, Alhaji Nasir Isa Kwarra, a ranar Alhamis da ta gabata, ya yi tsokaci kan yadda aka kashe Naira biliyan 224 da Gwamnatin Tarayya ta fitar, domin gidanar da ƙidayar gidaje da yawan jama’a a shekarar nan ta 2023.

Kuɗaɗen farko da aka ware domin gudanar da atisayen sun kai Naira Biliyan 800, amma an ɗage bayan ɗage babban zaɓe ƙasa.

Isa Kwara ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wani taron karin kumallo da wasu zaɓaɓɓun shugabannin kafafen yaɗa labarai cewa, “an kashe Naira biliyan 224 wajen shirye-shiryen gudanar da atisayen da suka haɗa da buga takardu, horar da ma’aikata da dai sauransu.”

Idan za a iya tunawa, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ɗage ƙidayar jama’a bayan ganawa da dama da masu ruwa da tsaki a ƙarshen watan Afrilu, 2023.

Ya ce, gwamnatin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, ce za ta yanke ranar da za a gudanar da ƙidayar ƙasar.