Ba za mu amince da hatsaniya ranar rantsar da Gwamnan Kano ba – CP Gumel

Daga RABIU SANUSI a Kano

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ƙarƙashin kwamishinanta CP Muhammad Usaini Gumel ta tabbatar da cewa ba za ta amince dukkan wani nau’i na kawo tashin hankali ko tarzoma a bikin rantsar da gwamnan jihar Kano a ranar 29 ga watan Mayun nan da sauran ‘yan majalisar jiha da tarayya.

Wannan batun na zuwa ne a wata sanarwa da Kakakin Rundunar SP Abdullahi Kiyawa ya raba wa manema labarai a ranar Talatar nan da ta gabata.

Sanarwa tabce kwamishinan ya kuma ja kunnen dukkan magoya bayan waɗannan jam’iyyu da iyayen gidansu kan batun tsatsauran ra’ayi na siyasa don su janye wannan mummunar aƙidar ta su.

CP Usaini Mohammed Gumel ya kuma ƙara da cewa dukkan masu niyyar yi wa jihar Kano zagon ƙasa da su ƙoƙarta janye wannan ra’ayi nasu.

Usaini Gumel a cikin sanarwar ya ci gaba da cewa za su cigaba da gudanar da aiki a dunƙule da sauran jami’an tsaro don tabbatar da kwanciyar hankali da kare kadarorin jama’a da gwabnati tare da ganin an samu nasarar gudanar da bikin rantsar da gwamnan jihar Kano mai jiran gado da sauran ‘yan majalisar jiha da wakilai cikin ƙoshin lafiya.

“Mun lura da gudanar da bikin rantsar da gwamnan wani abu ne mai tarin muhimmanci da kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanadar don ɗorewar tsarin siyasar mu a matsayin ƙasa ɗaya al’umma ɗaya.

Don haka ita ma rundunar ‘yan sanda ta ce tana da haƙƙin kare domukuraɗiyya da bin diddigin tsarin mulkin ƙasa.”

Sanarwa ta ce kwamishinan ya cigaba da bayyana dokar ƙasa da tsarin mulki ya ba ‘yan sandan ƙasa damar tabbatar da ingantaccen tsaro kamar yadda sukan yi a lokacin zaɓe.

Don haka ne ma ya ce yana ganin hakan ya haifar da zaɓaɓɓun ‘yan takara da kuma bada goyon baya ga bukin rantsar da su cikin nasara, inda daga ƙarshe ya bada tabbacin gudanar da wannan aiki babu sani ba kuma sabo.