Za a yi ƙidayar jama’a a 2025 – NPC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Hukumar Ƙidayar Jama’a ta Ƙasa (NPC), Alhaji Nasir Isa Kwarra, ya sanar da cewa, za a gudanar da ƙidayar jama’a a Nijeriya a 2025. 

Kwarra ya bayyana hakan yayin bikin cika shekara guda na Taron Nairobi kan ƙidaya da Cigaban Al’umma (ICPD) a Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja, jiya Alhamis. 

Duk da shawarar Majalisar ɗinkin Duniya na cewa, a gudanar da ƙidaya duk bayan shekaru 10, Nijeriya ta yi ƙidayar ƙarshe ne a 2006. 

Gwamnatin tsohon Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da ta gabata ta ɗage ƙidayar a 2023, inda ta nemi gwamnatin da ta ci zaɓe a 2023 ta jagoranci aiwatar da aikin ƙidayar. 

Kwarra ya jaddada cewa jinkirin gudanar da ƙidayar na kawo cikas, musamman wajen tsara shirye-shirye da rabon albarkatun ƙasa a yankunan karkara. 

Ya ce, rashin aiwatar da sahihiyar ƙidaya na hana isar da ayyukan kiwon lafiya yadda ya kamata, wanda ke haifar da mutuwar mata masu juna biyu da ƙananan yara. 

“Muna da niyyar inganta lafiya musamman a ɓangaren haihuwa, kawar da cin zarafin jinsi, da tabbatar da an ba mata da matasa damarmaki,” a cewar Kwarra. 

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC), ta ce, ta tanadi duk abinda ya kamata domin gudanar da ƙidayar jama’a da gidaje. 

Kwamishinan NPC a Adamawa, Clifford Zirra, wanda ya bayyana hakan, ya ce, umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kawai hukumar ke jira, domin fara ƙidayar.

By ukarofi