Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Rana ce ta farin ciki da annashuwa ga al’ummar garin Gwagwarwa, sakamakon naɗin sarauta da Mai Girma Dagacin Gwagwarwa, Alhaji Usman Sanusi Aliyu, ya yi wa Barista Ibrahim Isah Aliyu a matsayin Matawallen Gwagwarwa, wani mataki da ake ganin zai ƙara haɗin kai da martabar sarauta a yankin.
Barista Ibrahim Isah Aliyu Matawallen Gwagwarwa ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da ’yan jarida jim kaɗan bayan kammala bikin naɗin sarautar da aka gudanar a garin.
Ya ce tun kafin naɗin sarautar, yana daga cikin mambobin ƙungiyar raya garin Gwagwarwa, inda suke haɗa kai da sauran al’umma domin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da bunƙasar cigaban yankin.
Matawallen Gwagwarwa ya nuna cewa garin Gwagwarwa na ɗaya daga cikin wuraren da ke tattare da ƙabilu daban-daban daga sassan ƙasar nan, amma duk da haka ana rayuwa cikin zaman lafiya, ana auratayya, kuma al’umma sun zauna tamkar ’yan’uwa ɗaya.
Barista Ibrahim Isah Aliyu ya miƙa godiyarsa ga Dagacin Gwagwarwa, Alhaji Usman Sanusi Aliyu, bisa wannan karamci da ya nuna masa na ba shi sarauta, inda ya yi alƙawarin kasancewa mai biyayya da ba da gudunmawa wajen bunƙasa cigaban yankin da martabar masarauta.
Haka kuma, ya gode wa ’yan’uwa, abokan arziki da dukkan jama’ar da suka halarci bikin domin taya shi murnar wannan sarauta, tare da roƙon su da su ci gaba da yi masa addu’a domin Allah Ya ba shi ikon sauke nauyin da aka ɗora masa yadda ya kamata.
