Zamfarawa mazauna Kano sun yi taro a karon farko

Manhaja logo

Daga MUHAMMAD MUJITTABA a KANO

Ƙungiyar Zamfarawa mazauna Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Kabir Ibrahim Gusau, ta gabatar da gagarumin taro wanda ya haɗa da ɗimbin Zamfarawa mazauna Kano daga sassa daban-daban na ƙananan hukumomin Kano har da maƙwabtan jihohi.

Taro ya gudana ne a ranar Asabar a Birnin Kano.

A jawabinsa, Shugaban Ƙungiyar Alhaji Kabir Ibrahim Gusau ya ce maƙasudin wannan taro shi ne sa da zumunci a tsakanin waɗannan al’ummar Zamfara mazauna Kano da kuma qundirin tallafawa juna ta fuskoki daban-daban na rayuwa da kuma yunquri na ganin al’ummar Zamfara mazauna Kano da ma sauran jahohi sun haɗa kai da gwamnatin Zamfara da sauran masu ruwa da tsaki na ganin an warware matsalolin Zamfara da kuma samar da cigaba ta kowacce fuska musamman ba da shawarwari da addu’o’i na alkairi ga al’ummar Zamfara dama Nijeriya baki ɗaya.

Daga cikin manyan baƙi da su ka halacci wannan taro da sanya albarka akwai kwamandan hukumar ba da kariya ga farar hula na jihar Kano Alhaji Muhammad Lawan Falala na NSCDC na kano kuma ɗan asalin jihar Zamfara mazaunin kano wanda ya bayyana mahimmacin wannan taro da kuma irin gudunmawar da su ke bayarwa na ganin an sadar zumunci da taimakon juna da wannan al’ummar ta Zamfarawa mazauna Kano.

Haka shi ma Alhaji Aminu Tsohon mai bawa tsahon gwamnan kano shawara akan aiyuka na musamman ya bayyana jin daɗinsa da yadda wannan taro ya guna kasancewar Kano da zamfara ’yan uwan juna ne ta mu’amala, kasuwanci, da auratayya da sauran al’amura na fahimtar juna a tsahon shekara da shekaru.

A qarshe, ɗaya daga cikin shahararru masana a harshen hausa a duniya da ke shashin harsuna na jamiar Bayero kano Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau, da Dakta Ahmad Gusau sun bayyana cewa wannan taro da wannan ƙungiya sun sha bambam da sauran ƙungiyoyi irin waɗannan da su ka gabata dan haka akwai kyakkyawan fata wajan cigaban alummar Zamfara mazauna Kano da ma sauran jahohin Najeriya.

Sai kuma takwaransa Farfesa Gusau daga sashin kimiyar siyasa na jami`ar bayero da shi ma yayi fatan alkairi da wannan ƙungiya ta su ta Zamfarawa mazauna Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *