Ƙungiyar Dillancin Man Fetur a Nijeriya ta ‘Depots and Petroleum Products Marketers Association of Nigeria’ (DAPPMAN) ta yi alƙawarin samar da manyan motocin bas 100 don tallafa wa yunƙurin gwamnati na cire tallafin man fetur.
Da take magana bayan ganawarsu da Shugaba Bola Tinubu ranar Laraba, shugabar ƙungiyar Dame Winifred Akpani ta ce suna goyon bayan matakin gwamnati na cire tallafin 100 bisa 100.
Akpani ta ce motocin ƙirar gida ne kuma masu amfani da iskar gas maimakon fetur.
“Cire tallafin mai ba ya nufin tsawwala farashinsa ko kuma rage yawansa a tsakanin ‘yan Nijeriya,” in ji ta. “Magana ce ta yin abin da ya dace game da tallafi a harkokin man fetur.”
Tun farko gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago a Nijeriya sun shirya tsunduma yajin aikin gama-gari amma daga baya suka janye bayan su gana da shugaban ƙasa.