Ranar Dimokuraɗiyya: Ku ƙara haƙuri da halin da ƙasa ke ciki, ina jin abin da kuke ji, cewar Shugaba Tinubu ga ‘yan Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi ‘yan Nijeriya da su ƙara haƙuri game da halin da suka tsinci kansu sakamakon cire tallafin mai, yana mai cewa, yana jin abin da ‘yan ƙasar ke ji.

Tinubu ya yi wannan roƙo ne a ranar Litinin da safe a jawabinsa ga ‘yan ƙasa albarkacin Ranar Dimokuraɗiyya ta bana.

Bana shekara 30 kenan cib da samuwar wannan rana ta “June 12”, wadda ta samo asali sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa da aka gudanar a shekarar 1993.

Zaɓen da aka tabbatar da marigayi Chief Moshood K. Abiola, shi ne wanda ya lashe amma daga bisani Shugaban Ƙasa na wancan lokkaci ya soke zaɓen.

Tinubu ya ce juriyar da ‘yan Nijeriya suka yi ba za ta faɗi ƙasa banza, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta bambaɗa musu ababen more rayuwa masu yawa domin inganta musu rayuwa.

Shugaban ya duk da dai ya san matakin janye tallafin man zai jefa ‘yan ƙasa cikin wani hali, ya ce hakan shi ne abin da ya kamata a yi domin samar wa gwamnati da ƙarin kuɗaɗen da za ta yi wa ƙasa aiki yadda ya kamata.