Dandalin shawara: Mijina na yawan kamanta ni da mahaifiyarshi

Daga AISHA ASAS

(Ci gaba daga makon jiya)

TAMBAYA:

Ba ni shawara Asas don Allah. Maigidana na yawan cewa, Ina kama da mamatai. Ba fa fuskata da fuskarta ba, har ga jiki. Yana cewa wai idan na juya Ina tafiya sai in yi kama da ita. Idan yana son ɓata min ma sai ya ce ko fita muka yi sai an ɗauka ni mamatai ce ba mata ba. Idan aka jima bai ba ni haƙƙina ba, sai na yi magana, zai iya cewa, wai wani lokaci yana kunyar kusanta ta saboda kama da surrar jikina ke yi da ta mamatai. Abin ya ishe ni wallahi. Ga shi ni ba wata babba ba da za a ce ta tsufa, haihuwa biyu kawai fa Asas.

AMSA:

Shin wacce sura ce wannan?

Idan muka buɗe littafi mai tsarki, muka kai kallo ga suratul Mujadala, tun daga aya ta farko Allah maɗaukakin sarki ya ce, “Lalle Allah Ya ji maganar wadda ke yi maka jayayya game da mijinta, tana kai ƙara ga Allah, kuma Allah na jin muhawararku. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani.”

A aya ta biyu, Allah (S W.A) Ya bayyana wannan hukunci da kuma kiransa da suna ‘zihari’ kamar yadda muka faɗa a baya, inda Ya ce, “Waɗanda ke yin zihari daga cikinku game da matansu, su matan nan ba uwayensu ba ne, babu uwayensu face waɗanda suka haife su. Lalle su, suna faɗar abin ƙyama na magana da ƙarya, kuma lalle Allah haƙiƙa Mai yafe wa ne, Mai gafara.”

A aya ta uku dukka dai a wannan sura ta Mujadala, Ubangijin bayi, Ya bayyana hukuncin da ya hau wuyan wanda ya aikata hakan, abinda zai aikata kafin ya iya dawo wa matarshi. Ma’ana idan ka yi irin wannan furucin, a Musulunce ka haramtawa kanka matar, kuma idan daga baya ka buƙaci lashe aman da ka yi, ko ka so kusantar matarka da ka siffanta jikinta da na mahaifiyarka, to fa akwai ladabtarwar da za ka yi, wadda zata sake halasta ma matar.

Allah Mai girma Ya ce, “Waɗanda ke yin zihari game da matansu, sa’annan su koma wa abin da suka faɗa, to, akwai ‘yanta wuya a gabanin su shafi juna.Wannan ana yi muku wa’azi da shi. Kuma Allah Mai ƙididdigewa ne ga abin da kuke aikatawa.”

‘Yanta baiwa ce hukuncin da ya hau kanka idan ka yi wa matarka irin wannan, sannan ka yi muradin dawowa gare ta. Sai dai akwai zaɓi na biyu ga wanda bai da halin ‘yanta baiwa, kuma zaɓin da za mu iya cewa a wannan zamani ya zama abinda za a iya yi, kasancewar sha’anin bayi a yanzu na da rikitarwa, wanda malamai da dama sun tabbatar da babu bayi a yanzu.

Zavin kuwa shi ne, azumi sittin, wato na wata biyu a jere, ko kuma idan yana tare da matsalar da zata iya hana shi yin azumin, to zai ciyar da mabuƙata sittin. Kamar yadda Allah Maɗaukakin sarki ya faɗa a cikin aya ta huɗu ta suratul Mujadala, cewa, “To, wanda bai samu ba, sai azumin wata biyu jere a gabanin su shafi juna, sa’annan wanda bai sami ikon yi ba, to, sai ciyar da miskinai sittin. Wannan domin ku yi imani da Allah da Manzonsa. Kuma waɗannan hukunce- hukunce haddodin Allah ne. Kuma kafirai, suna da azaba mai raɗaɗi.”

Kinga kenan tun a lokacin da ya fara furta miki wannan maganar, yayin da ya dawo ku ka tafka kuskure. Shi bai san abinda yake kansa ba, don haka ya ɗauka kamar da wasa, ke kuma ba ki sani ba bare ki sanar da shi, don haka ya ci gaba da faɗa yana maimaitawa, don bai ɗauka tana iya zama shamaki gare shi ga jikinki ba.

To a wannan gava, zan iya cewa, na hango ababe biyu zuwa uku, abu na farko ba na jin abinda ku ka yi na baya zai ci gaba da zama tabo gare ku, sakamakon kun aikata ne bisa rashin sani, domin manzon rahma ya ce, “an yi rangwame ga mutane uku, wanda ya aikata abu bisa rashin sani, da wanda ya yi bisa rashin hankali, da kuma wanda aka tursasashi ya aikata.”

Ma’ana laifin da ka aikata bisa ga ba ka san laifi ba ne, ko kuma mahaukacin da zai aikata savo cikin haukar, da kuma mutumin da aka aza wa wani makami aka tilasta shi faɗa ko aikata wani savo, to ba laifi don ya aikata. Kenan abinda ku ka yi bayan furucin mijinki zai iya hawa kan wannan.

A wani ɓangare tambayar da za ku yi wa kanku ita ce, me ya hana ku sanin? Shin ƙarancin inda za ku nemi ilimin addini ne ko kuwa ganganci ne da rashin ba wa ilimin addini muhimmanci? A nan kinga kuna da laifi dukka, sai dai wannan tsakanin ku da Ubangijinku ne. Ku nemi gafararShi da niyyar gyarawa.

Idan mun koma kan mataki na biyu, wato me ya kamata ki yi yanzu da ki ka sani, a nawa gani, kina buƙatar sanin ko matakin da ki ke kai na rashin sanin hukuncin abin shi ma mijin haka ne, ma’ana ya san da hukuncin ko shi ma cikin duhun kai yake yi.
Idan da sani yake yi, to wannan hukuncin ya tabbata a wurin sa, ma’ana sai ya yi azumi sittin ko ciyar da mabuƙata sittin.

Idan kuwa a duhun kai yake yi, zan iya cewa, a tuntuɓe malamai kan wannan, domin samun hujja tare da amsar, domin ba ni da wani hukuncitsayayye da ke da ‘isnadi’ mai nauyi da ya yi magana kan wannan, sai dai idan zan yi amfani da hukuncin wanda ya yi laifi bisa rashin sani. Amma a wurin malamai za a samu bayani mai gamsarwa.

Da wannan muka kai ga zance na ƙarshe, wato neman shawarar da ki ke yi. Kusan zan iya cewa, Alƙur’ani ya sanar da ke komai, abinda kawai zan ce shi ne, mataki na farko, ki fara da tuntuɓar maigidanki kan lamarin, ki fahimci ko ya san abinda yake aikatawa laifi ne. Idan ya sani, kamar yadda aka faɗa a baya, za ki ƙaurace masa, ki kuma tabbatar masa sai ya aikata hukuncin da Allah Ya shar’anta kafin ki dawo gare shi. Wannan zai iya kai ku ma da ki kai ƙarar shi ga magabata idan abin ya fi ƙarfin ki.

Idan kuwa kin fahimci aikin jahilci ne, to ki yi masa bayanin da aka yi ma ki, idan ya ɗan fahimta sai ki ba shi shawarar ku ɗunguma ku kai kanku gaban malamin Allah da ke faɗa bisa ilimi, shi zai ƙara wanke ƙwaƙwalwarku da kuma sanar da ku mafita daidai da faɗar addini.

Daga ƙarshe zan ba ki shawarar ki koma makaranta ko da ta dare ce da ake yi don matan aure. Ki daure ki dinga zuwa, ko ki nemi maigidan naki ya samo ma ki mai zuwa gida ta koyar da ke. Saboda zama a hakan ba zai haifa ma ki ɗa mai ido ba, kin dai ga misali da wannan tambaya da ki ka yi, ba ki san me gobe zata haifar ba.

Kada ki zauna a duhun kai har ki dinga aikata laifukan da za su iya fitar da ke Musulunci, kuma ba ki da dalilin kare kanki a gaban Ubangiji, saboda dai ilimin ya wanzu, ke ce dai ba ki neme shi ba.

A wannan zamani da samun ilimi ya sawwaƙa, hanyoyin samun sa suka yawaita, ba na jin jahili na da kalmar kare kansa a gaban mahaliccin sa.

Allah Ya ba mu ilimin da zai amfane mu duniya da lahirar mu.