Galibin motocina da aka kwashe na mallake su tun kafin in zama gwamna – Matawalle

Daga BASHIR ISAH

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya bayyana cewa, galibin motocin da jami’an tsaro suka kwashe a gidajensa da ke Gusau da Maradun ya mallake su tun kafin ya zama gwamna.

Matawalle ya faɗi hakan ne yayin da yake maida martani game da mamaye masa gidaje da ‘yan sanda da DSS suka yi a ranar Juma’a.

A hirar da BBC Hausa ta yi da shi a ranar Asabar, Matawalle ya zargi jami’an tsaron da wawushe kayan matansa da na yaransa ciki har da suturunsu.

Ya ce babu wani umarnin kotun da aka isar masa na halasta wa jami’an tsaron shiga gidajen nasa kamar yadda magajinsa Dauda Lawal ya yi iƙirari.

“Ina harkar sayar da motoci da daɗewa, kuma galibin motocin da jami’an tsaro suka kwashe a gidajena motoci ne da na sayo daga Amurka tun kafin ma in zama gwamna,” in ji Matawalle.

Ya ƙara da cewa, motocin da aka kwashe a gidansa na Maradun, abokan arziki ne suka ba shi gudunmawarsu kuma baki ɗayansu suna ɗauke da hotonsa tare da Shugaban Ƙasa Tinubu.

Kazalika, ya ce ya kamata jami’an tsaro su baje motoci 40 da suka ce sun gano a gidajen nasa kamar yadda suka yi iƙirari don jama’a su gani su kuma yi alƙalanci.

Ya ce duk wanda ya san Matawalle, “Ya san ni da harkar motoci tun kafin in zama gwamnan Jihar Zamfara.”

Haka nan, ya ce ba zai buƙaci jami’an tsaro ko gwamnatin jihar su dawo da motocin ba, amma “Zan bi hanyar da ta dace kamar yadda doka ta shimfiɗa.”