Rage daraja ko daidaita canjin Naira?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Kafin na yi nisa a rubutun nan kowa ya san yadda darajar Naira ta yi ƙasa har a wani lokaci a bara Nairar ta doshi Naira 1000- kan dalar Amurka ɗaya a kasuwar canjin kuɗi. Hakanan a ma canjin gwamnati hukumance Naira kimanin Naira 460 ke matsayin dala ɗaya da a ke amfani da hanyar wajen hada-hadar kasauwanci ko wasu buƙatu da kan haɗa ’yan Nijeriya da su ka samu dama da ƙasashen ƙetare.

Dala ta zama kuɗi mai muhimmanci da attajiran Nijeriya ke amfani da ita wajen gudanar da lamuransu hakanan ’yan siyasa ma kan yi amfani da dala wajen tura saqonni cikin sauqi. Dala a cike da aljihun babban riga za sui ya kai wa yawan Nairar da sai an cika buhu a samu ɗan dako ya ɗauka. Ba mamaki yadda dala kan vuya ko ma a kasa samunta a bankuna a duk lokacin da a ke tsakiyar siyasar zaɓe.

Hatta a wannan zaɓen na 2023 nan da ya gabata dala ta nemi ɓacewa bat daga bankuna don yadda a ka ɓoye ta wa imma don siyasa ko kuma don adana maƙudan kuɗi a waje ɗaya gabanin tashi amfani da kuɗin in an samu lafawar harkar siyasa ko ta sa ido. Don haka ba zai zama daidai ba mutum a duk inda ya ke a Nijeriya ya na aikin gwamnati ko ba ya yi ya ce ba abin da ya haɗa shi da dala. Kowa na da hannu ko lamarin tashin dala ya shafe shi.

Wato a nan za a fahimci cewa a kan yi amfani da dala wajen shigo da man fetur da sauran kayan da jama’a ke amfani da su na yau da kullum aƙalla ma a cikin miya! Duk lokacin da dala ta qara tashi ko man fetur to nan take a kasuwanni za su amsa da ƙara farashin kaya.

Abun takaici kuma shi ne ba ranar da za ka ji don an samu sauƙi ya zama kasuwa ta sauko da farashi. Dalilin tashin dala fa wasu kayan sun ninka farashi har sau biyu ko sau uku. Wannan ya sa wasu ke kiran ƙayyade farashi ko kuma zuba ido kan farashin kayan da mutane su ka fi buƙata. Ita tsada kan sake juyowa ta shafi kayan da mutane ke samarwa a cikin gida misali kayan amfanin gona su kan cilla sama don tsadar takin zamani wanda shi ma dala kan shafe shi a wajen yin oda.

Masana tattalin arziki na cewa hanya mafi sauƙi ta samar da daidaiton farashi ita ce sarrafa akasarin kayan da ’yan ƙasa ke buqata a cikin gida don haka ba babbar buƙatar sai an nemi canjin dala ko wasu kuɗin ƙasashe masu cigaban masana’antu don shigo da kayan daga ƙetare. Ya kamata a ce kowace jiha na da wata masana’anta da kan samar da abun da ’yan ƙasa ke buƙata don dakatar da shigowa da hajoji daga ƙetare.

Misalin kamfanonin akwai na sarrafa tumatur, mulmula ƙarfe, sarrafa shinkafa ta tsira daga tsakuwa, lemon kwalba, dardumar sallah ko ta adon ɗaki da sauarn su da dama. Samar da irin waɗannan hanya ce mai kyau wajen sauko da farashin kayan masarufi da kuma a lokaci guda samar da aikin hyi ga ɗimbin matasa.

Maimakon gwamnati ta ƙarfafa tafiya ketare da dala wajen sayo kayayyaki, ta na iya gayyato kamfanonin da kan aera kayan irin na kimiyya su zo Nijeriya su buɗe kamfanonin. Idan kamfanin ƙetare ya buɗe reshensa a cikin Nijeriya ya zama wajibi ya yi amfani da Naira don haka Naira za ta yi daraja. Masu sarin kaya ba za su buƙaci dal aba sai dai Naira don sayo kayan da za su samu riba.

Buɗe matatar fetur a Legas da a ka fara yi na da amfani ainun don ya nuna nan gaba kaɗan za a iya samun duk man da a ke buƙata a cikin gida. Kuma wannan tamkar buɗe hanya ce ta wasu manyan ’yan kasuwa su buɗe wasu ƙananan matatun a wasu sassan ƙasar.

Hakazalika indai har gwamnati ba za ta iya gyara matatar mai ta Fatakwal, Warri ko Kaduna ba, to ta miqawa ’yan kasuwa su zuba jarin su don farfaɗo da su. Kun ga ai ɗan kasuwa ba zai bari ya zuba kuɗinsa sannan ya bari ya yi asara ba. Ɗanyen man fetur dai akwai shi a Nijeriya ga shi nan ma a na ƙara gano shi a wasu sassan arewa.

Babban Bankin Nijeriya, CBN ya daidaita canjin Naira a tsarin shigowa da kuma buƙatun fita ƙetare.

Bankin ya ƙi amincewa da hakan a matsayin rage darajar Naira. Fitowar labarin ya sa an ƙalubalanci bankin da cewa kai tsaye ya rage darajar Naira ne amma ya fito ya ce ba haka tsain ya ke ba.

Wannan ya biyo bayan jawabin shugaba Tinubu a wajen rantsarwa na daidaita farashin canji don dacewa da yanayin kasuwa. Shgaban kazalika a dai jawabin ne ya soke tallafin man fetur.

”Za mu daidaita canjin kuɗi ya tafi daidai da yanayin tattalin arziki ko kasuwar mu” Inji sabon shugaba Tinubu a jawabin da ya gabatar wanda bai zama abun mamaki ba da babban bankin ya motsa daidai da jawabin kamar yadda ya faru ga kamfanin man fetur NNPC da ya ɗane kan baka don tashin gauron zaɓin man fetur. Dama waɗannan sassan biyu masu muhimmanci a tattalin arzikin Nijeriya kan tafi daidai da muradun gwamnati mai ci ta yadda ta ke son tattalin arziki ya gudana.

Labarin da ya fito dai shi ne bankin ya cilla canjin na shigowa da fitar da hajako buƙatun ƙetare zuwa Naira 630

A nan babban bankin dai ya fito ƙarara ya ƙi amincewa da amfani da Kalmar rage darajar Naira kan matakin amma ya ce abun da ya faru daidaita lamuran ne bisa ga yanayin da zai taimaki tattalin arziki.

A nan jami’in labarun bankin Abdulmumin Isah ya fara ne da ƙaryata labarin da jaridar Daily Trust ta wallafa amma a larin bayaninsa ma’anar da bankin ke nufi ta fito fili.

”Mu na hana tashi da saukar farashin ne kawai shi ya sa CBN ya shigo don daidaita farashin kar ya riqa tashi sama ya na kuma saukowa ba jan akala” Inji Isah wanda ya ƙara nanata cewa hatta ranar da lamarin ya faru da sanyin safiya dalar na Naira 465 ne a wajen bankin ba fiye da Naira 600 ba.

Abun fahimta dai a nan bankin zai bar sha’anin ya zama tamkar kasuwa ta yi halin ta ne kuma ya rage tazarar canjin da na kasuwar bayan fage don in an yi hakan zai toshe ribar masu sayan dala da zummar fita don lamuran da za su taimaki tattalin arziki sai su sayar don cin ƙazamar riba. Kazalika daidaita canjin zai ƙarawa masu zuba jari ƙwarin guiwa su shigo Nijeriya don yin harkokinsu.

Masana tattalin arziki sun ce bambancin canjin gwamnati da na bayan fage na firgita manyan ’yan kasuwar duniya wajen buƙatar shigowa Nijeriya don kafa cibiyoyinsu. Ko ma dai me zai faru sai a jira zuwa wasu watanni ko zuwa ƙarshen shekarar nan don ganin irin tasirin da matakin zai yi.

Masanin tattalin arziki Abubakar Ali ya ce, duk matakin da za a ɗauka in ba a rage almubazzaranci ba ba za a samu nasara ba. Ali ya ce za ka ga ma’aikata ko wata cibiyar da ba ta samawa gwamnati ko sisin kobo amma jagororin ta na hawa manyan motoci biyu zuwa uku ko yin rayuwa ta sharholiya.

Za a zuba ido a ga yanda za ta kaya nan gaba kaɗan daga masu buƙatar dalar a hukumance da yadda hakan zai yi tasiri a kan farashin kayan masarufi.

Masanin tattalin arziki Yushau Aliyu ya kawo labarin wasu kamfanonin ƙetare da kan yi aiyukan kwangila a Nijeriya amma a wajen biyan su kuɗi sai su buƙaci dala. Don magance wannan masanin ya ba da shawarar a tilasta irin kamfanonin su riqa karɓar Naira don hakan ma na daga hanyar farfaɗo da daraja.

Tsohon shugaba Buhari ya taɓa nuna takaici ainun a wani faifan bidiyo da ya zaga kafin ya hau karagar mulki a 2015 kan batun rashin darajar Naira in da ya ke tambayar shin Nairar da ta ke aljihun ɗan Nijeriya na da daraja? I-lia kuma Allah ya jarrabi gwamnatin sa inda Nairar ta yi ta faɗowa fiye da duk yadda ta tava yi a tarihin Nijeriya. Naira tun ta na qasa da Naira 200 sai da ta doshi Naira 1000 ƙarƙashin mulkin Buhari. Shin Bola Tinubu na iya farfaɗo da darajar Naira da hakan bai samu ba a wajen magabacinsa Buhari?

Kammalawa;

Gaskiya sai mutane sun koyi da tsimi da tanadi a ɗan tsakanin nan don samun rayuwa mai dama-dama. Gujewa almubazzaranci ya zama mai muhimmanci tsakanin jama’a. Hakanan masu ɗan ƙarfi su riƙa duba makwabta da sauran ’yan uwa da abokai wajen tallafawa don a gudu tare a tsira tare. Ya kamata ita kuma gwamnati ta zaƙulo hanyoyin sauƙi da kuma rage farashin litar mai zuwa daidai gwargwadon yadda kowa zai ci riba ba tare da tallafin ba tsakanin gwamnatin, ’yan kasuwar fetur da kuma musamman talakawan ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *