Zan kawo wa Tinubu Kano kaf ɗinta a zaɓen 2027,  inji Minista Ata

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sabon ƙaramin Ministan Gidaje da Raya Birane, Yusuf Abdullahi, ya sha alwashin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

Ministan na wannan kalamai ne a yayin ganawarsa da manema labarai bayan dawowarsa Kano daga Abuja a ranar Lahadi.

Ya yi alƙawarin jajircewa wajen yayata ayyukan da shugaba Tinubu ke yi na sabunta fatan ‘yan Nijeriya.

Sannan ya jaddada aniyarsa ta cicciɓa aikin samar da gidajen da gwamnatin shugaba Tinubu ke yi tare da gode wa shugaban bisa karrama shi da wannan muƙami da ya yi.

Ministan ya yi alƙawarin tabbatar da nasarar jami’iyyar APC a Kano domin kuwa mutanen Kano sun samu wakilcin da ya kamata.

“Da yardar Allah za mu kawo wa shugaba Tinubu Kano a shekarar 2027,” in ji Abdullahi.

“Wannan muƙami da aka ba ni yana da nasaba da muhimmancin siyasar Kano ta tsakiya wacce ke da tarin ƙuri’u. Don haka, zan cigaba da wakiltar mazaɓata da ƙarfafa tafiyarmu ta siyasa.

Ministan ya ce ayyukan da ake kan yin su a ma’aikatarsa musamman waɗanda suka shafi shirin sabunta fatan al’umma, ayyuka ne masu muhimmancin gaske.

Sannan ya nuna cewa wannan nauyi da aka ɗora masa ba sabon abu ba ne a wajen sa, idan aka yi la’akari da cewa a baya ya riƙe muƙamin shugaban majalisar dokoki da shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Kano.

Ya ce Kano ta tsakiya ta fi kowanne yanki na Kano yawan ƙuri’u saboda ita ce ke da kaso 65% na masu rajistar katin zaɓe, sai dai yankin ba shi da wani wakilci a gwamnatacce.

“Amma ba shi yanzu shugaba Tinubu ya naɗa ni kuma sun bayyana ƙarfin guiwarsu a kaina saboda gogewar da nake da ita na zama dan majalisa tun 1999,” in ji ministan.

“Na taɓa zama shugaban majalisar dokokin Kano da zama mashawarci na musamman ga gwamma. Don haka yana ina da tabbacin za mu kawo Kano,” ya bayyana.

Jihar Kano dai na ƙarƙashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf ne na jam’iyyar NNPP wacce ta samu mulki a shekarar 2023 bayan kayar da ɗan takarar jami’iyyar APC.

Kamar yadda al’adar mulki take, kowanne gwamna musamman wanda yake kan tenuwa ta farko, yakan nemi tazarce kuma haka ake sa rai zai faru a 2027.

Wannan ta sa ƙila jami’iyyar APC fara ɗaura ɗamarar ganin ta ƙwace mulki daga hannun NNPP a zaɓen na 2027.

By ukarofi