Ƙasashe 51 sun haramta amfani da kuɗin Kirifto

Daga AMINA YUSUF ALI

Duk da irin shuhurar da tsarin samar da kuɗi ta hanyar cinikayyar sulalla ta yanar gizo, wato Kirifto Karansi ko Bit Koyin har yanzu ya kasa samun cikakkiyar karɓuwa a duniya. A halin yanzu bincike ma ya shaida cewa, yawan ƙyamatar Kirifto ya ƙara ninkuwa ne a ‘yan shekarun nan ma fiye da duk shekarun baya.

Tun a shekarar 2018 ne dai da ma aka samu adadi mai tsoka na ƙasashen Duniya waɗanda suka haramta amfani da tsarin kuɗin a cikin ƙasashensu. Inda jimillar ƙasashen da suka soke Kirifto ɗin suka kai 42 wato bayan da ƙasashen Misra, Iraqi, Ƙatar, Oman, Maroko, Algeriya, Tunisiya, Bangaladash, da kuma ƙasar Chana suka shiga sahu. 

 A halin yanzu sakamakon bincike daga babban laburaren majalisar dattawa dake Amurka ya bayyana cewa, abinda ake nufi da haramta amfani da Kirifto ɗin shi ne, duk wanda aka kama yana ta’ammali da shi, to za a ayyana shi a matsayin mai laifi kuma zai fuskanci hukunci a wajen hukuma. 

Laifuffukan sun haɗa da, canjin kuɗi ta hanyar amfani da Kirifto, buɗe bankunan ko cibiyoyin  hada-hadarsa, ko kuma yin ayyuka ga masu hada-hadarsa.

Jaridar ‘Nairametrics’ ta rawaito cewa, a watan Nuwambar 2021 ne dai ma wasu ƙasashen suka fara fitar da tsare-tsare a kan yadda za a tafiyar da halastacciyar hada-hadar Kirifto, ta hanyar samar da haraji, dokokin da suka shafi harajin, daƙile harƙallar kuɗaɗe da hana karkatar da kuɗaɗe izuwa tallafa wa ta’addanci.

Ƙasashen Turai dukkansu sun amince sai dai banda ƙasar Bulgeriya ita ta ƙeƙasa ƙasa. Inda wata majiya daga Ƙasar Faransa ta bayyana cewa, duk munanan abubuwan da ake yaɗawa game da Kirifto, shaci-faɗi ne kawai. 

Sai dai duk da wannan jajircewa da ƙundumbalar wasu ƙasashen, wannan bai sa ƙyamar ta Kirifto ta ragu ba. Don a halin yanzu ma ƙasashe da dama suna ƙoƙarin samar da kuɗi na bai-ɗaya a yankunansu.

Wannan shi ne zai sa a ƙara samun ƙaruwar ƙasashen da za su soke amfani da Kirifton a wannan shekarar ta 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *