Daga CMG HAUSA
Ƙasar Sin da mahukuntanta sun sha nanatawa a dandaloli da taruka daban-daban cewa, a kullum buri da manufar ƙasar Sin, shi ne tabbatar da ci gaba da zaman lafiyar duniya baki ɗaya, sabanin yadda wasu ƙasashe ke kallonta da ma yada jita-jitar cewa, ci gaban ƙasar Sin, musamman ƙoƙarin da take na zamanantar da kanta, wai barazana ce ga duniya.
Har kullum ƙasar tana fatan ƙasashen yammacin duniya, musamman Amurka da sauran ƙawayeta, za su kalli ci gaban ƙasar Sin, da ƙoƙarin da take na zamanantar da kanta da ido na basira, ta yadda za su dakatar da yada farfaganda maras tushe, ta ɗaukar wannan manufa da masu fashin baƙi ke cewa, za ta amfani duniya a matsayin barazana.
Sanin kowa ne cewa, hanya mafi dacewa ta warware duk wasu batutuwa da suka shafi ƙasashen duniya, musamman a wannan lokaci da duniya ke buƙatar zaman lafiya, adalci da ma abin da al’umma za su kai ga bakin salati, ita ce tattaunawa da dukkanin ƙasashe masu ruwa da tsaki, maimakon ware kai, da mayar da wasu saniyar ware, da gudanar da komai a bayyane, da damawa da kowa da kowa bisa daidaito da mutunta juna, tare da ci gaba da shawarwari da haɗin gwiwa, maimakon yada zarge-zarge marasa tushe.
Bugu da ƙari, shata layi saboda bambancin aƙida, da haɗa wata tawagar nuna wariya kan wasu ƙasashe, da yayata manufar ware kai tare da ’yan kanzagi, dukkaninsu sun sabawa aƙidun zamanin yau, kuma ba za su yi wata nasara ba. Hannu daya kuma, ba shi ɗaukar jinka.
Ya kamata irin waɗannan ƙasashe su san cewa, yanzu zamani ne na cuɗe ni-in-cuɗe ka, da martaba ka’idoji da dokoki na ƙasa da ƙasa da duniya ta amince da su, sabanin ƙoƙarin da wasu tsiraru ke yi, na nuna fin ƙarfi ko dannayi ko, safawa saura baƙin fenti, ko neman zama mai son ƙaƙaba wa sauran ƙasashe takunkumai da ƙa’idojin na tilas.
Don haka, ya dace a riƙa martaba zabin ƙasashe na samun bunƙasuwa, maimakon fakewa da wani batu na siyasa ko wata manufa da nufin cimma wata moriya ko neman tayar da zaune tsaye a sauran ƙasashe. Kowa da irin kiwon da ya karɓe shi….
Mai fassara: Ibrahim Yaya