Ƙalubalen yaran da ba sa zuwa makaranta

Dangane da ƙaruwar yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya, wanda a halin yanzu aka ƙiyasta su miliyan 20, Tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana lamarin a matsayin wani abu mai matuƙar tayar da hankali. A cewarsa, samun irin wannan adadi mai yawa na yara ba tare da tsarin ilimi ba, zai haifar da tarnaƙi ga ƙaruwar masu tada ƙayar baya da ’yan ta’adda a nan gaba.

Tsohon shugaban, wanda ya yi magana a wani taron ƙoli na ilimi na manyan makarantu na ƙasa da Majalisar Wakilai ta shirya, a wani ɓangare na ƙoƙarin magance ƙalubalen da ake fuskanta a fannin ilimi, ya nuna rashin jin daɗinsa da cewa ƙasar ta kasa yin taka rawar gani a cikin shirin “ilimi ga kowa” na duniya. Ya yi gargaɗin cewa Nijeriya za ta jefa makomarta cikin haɗari da irin waɗannan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Bai kamata masu kula da harkar ilimi su yi watsi da damuwar Obasanjo ba. Lallai wannan babban lamari ne a gare su da su fifita fannin ilimi musamman ilimin yaran Nijeriya. Mun faɗi haka ne saboda ƙasar nan ba za ta iya samun cigaba mai ma’ana ba yayin da miliyoyin yaro ke tanga-ri-ri a gari. Babu yadda za a yi waɗannan yara su taka rawar gani wajen gina ƙasa. Idan ba a kawo yaran ajujuwa ba, za su zama barazanar tsaro ga al’umma.

Wasu daga cikin abubuwan da ke haddasa ƙaruwar yawan yaran da ba sa zuwa makaranta sun haɗa da rashin tsare-tsare na qasa da kuma ƙaruwar yawan jama’a. Shi ya sa ya zama dole masu tsara tattalin arzikinmu su kula da ƙaruwar al’ummar ƙasa. Suna buƙatar aiki tuƙuru don sarrafa shi.

Ba a yarda da ƙaruwar adadin yaran da ke wajen tsarin makaranta ba. Abin farin ciki, muna da albarkatun da za mu shigar da waɗannan yara a cikin tsarin makaranta. Kafin sanarwar Obasanjo, Hukumar Kula da Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO), ta fitar da bayananta na duniya kan yaran da ba sa zuwa makaranta a watan Satumban 2021, sun nuna cewa Nijeriya na da kimanin yara miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta.

Idan aka yi la’akari da yadda ake fama da matsalar rashin tsaro a ƙasar nan, taɓarɓarewar tattalin arziki da ƙaura daga wuri zuwa wuri, tabbas adadin ya ƙaru.

Rahoton ya ci karo da ikirarin da Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya yi a watan Janairun 2021 na cewa adadin yaran da ba sa zuwa makaranta ya ragu daga miliyan 10.1 zuwa miliyan 6.9. Adamu ya yi ikirarin cewa yara miliyan 3.2 da ba sa zuwa makaranta, an shigar da su cikin shekara ɗaya da watanni bakwai, saboda wasu ayyuka da ma’aikatar ilimi ta tarayya ta yi.

Ƙalubalen rashin zuwa makaranta wani hatsari ne ga Nijeriya. Adadin miliyan 20 na wakiltar kashi 10 cikin 100 na al’ummar ƙasar. Halin da ya fi yawa a Arewa, shi ma yana iya haifar da tashe-tashen hankula, fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran ayyukan muggan laifuka. Wasu al’adun gargajiya na tarihi, waɗanda ke hana karatun yara, dole ne su ƙara tsananta barazanar.

Har ila yau, talauci wani abu ne da ke taimakawa wajen haifar da mummunan lamarin da kuma mummunar ɗabi’un iyaye na sayen dukiya fiye da ilimi. Domin magance ƙalubalen rashin zuwa makaranta, ya kamata gwamnatin tarayya da na jihohi su ɗauki lamarin a matsayin babban fifiko. Ƙarin kuɗaɗe ga fannin ilimi ya kasance kan gaba don bunƙasa fannin.

Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya yi ƙoƙari matuƙa wajen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta ta hanyar shirin makarantar Almajiri. Sai dai daga baya an yi watsi da wannan shiri na abin yabawa nan kafin Jonathan ya bar mulki.

Abin yabawa ne yadda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2023, ya gabatar da Naira tiriliyan 1.79 a fannin ilimi, wanda ya kai kusan kashi 8.8 na kasafin kuɗin na Naira tiriliyan 20.5. Muna fatan da wannan rabon, za a magance matsalar yaran da ba su zuwa makaranta a gaba.

Gargaɗin da Obasanjo ya yi abu ne mai ban tsoro kuma bai kamata a yi watsi da shi ba. Nijeriya na buƙatar vullo da wasu tsare-tsare masu ɗorewa domin farfaɗo da yaran da ba sa zuwa makaranta. Babu wani yaro ɗan Nijeriya da ya kamata ya fita tsarin ilimi. Ilimi wajibi ne ba ra’ayi ba. Ya kamata a sanya ilimin farko a jihohi 36 da qananan hukumomi 774 na ƙasar nan.

A bar gwamnati ta magance dodo na rashin tsaro tare da sanya halartar makarantu armashi ta hanyar ƙarfafa shirin makarantu. Ya kamata a fara kamfen na wayar da kan jama’a kan buƙatar yaran da ba su da tsarin makaranta su koma aji. Ya kamata a ƙarfafawa iyayen yaran kan muhimman ilimi, sannan kuma su riƙa barin ’ya’yansu zuwa makaranta.