2023: Emefiele ya nemi kotu ta ba shi damar tsayawa takara, duk da yana kan muƙamin gwamnati

Daga AMINA YUSUF ALI

Godwin Emefiele, Gwamnan babban Bankin Nijeriya (CBN) ya nemi Kotun Ƙoli ta Tarayyar Nijeriya dake a Abuja ta bayyana cancantarsa ta tsayawa takarar shuagabancin Nijeriya a kakar zaɓe mai zuwa ta 2023.

A kwanakin nan ne dai jagoran babban Bankin wanda ya daɗe yana musanta muradinsa na zama shugaban ƙasar Nijeriya a 2023, ya sa Naira Miliyan ɗari, N100,000,000 ya sayi fom ɗin neman takarar shugaban qasar a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

A lokacin da ya yi wancan jawabi nasa, mutane da dama sun yarda da shi. Domin suna da tabbacin cewa, da wuya a ce Gwamnan babban banki mai ci ya tsaya takarar muƙamin siyasa ba tare da ya bar gado ba.

Emefiele a cikin wata ƙara da ya shigar kafin bayyana muradinsa na takara inda ya nemi kotu ta yi wa hukumar zaɓe (INEC) da Antoni janar na tarayyar ƙasar nan birki a kan kada su hana shi tsayawa takara a zaven 2023 ba tare da ya sauka daga muƙaminsa na Gwamnan CBN ba.

A ƙarar da ya shigar mai lamba, FHC/ABJ/CS/610/2022 ya bayyana cewa, akwai wani hukunci da ya wuce sashe na 137(1) (g) da na 318 na kundin tsarin mulkin Nijeriya ta shekarar 1999 wacce ta bayyana cewa, duk wani mai riƙe da muƙamin gwamnati dole ya sauka, ko ya yi ritaya daga muƙaminsa aƙalla kwanaki 30 kafin a fara zaɓen shugaban ƙasa. Sai dai an bayyana cewa, akwai wani tanadi na dokar 2022 na sashe na 84(12) na dokar zaɓe a kundin tsarin mulkin Nijeriya wacce aka yi wa garambawul a shekarar 2022.

Dokar ta ba da dama ga ɗan takarar da zai iya tsayawa takara kuma ya shiga zaven cikin gida na jam’iyyarsa, sannan kuma yana da haƙƙin ya zaɓa kuma a zaɓe shi a kowacce irin jam’iyyar siyasa a ƙasar nan a ƙarƙashin kundin mulkin ƙasar nan (Da aka yi wa garambawul).

Duba da waɗannan bayanai, ana ganin ba za a iya dakatar da ɗan takarar ya zava ko a zaɓen shi a muƙamin siyasa ko na jam’iyya da ya yi niyya ba a Nijeriya. Kamar yadda aka rawaito a ƙarar da aka shigar.

Sai dai wata tambaya da aka gabatar gaban kotun dangane da ƙarar ita ce, shin ya kotun za ta yi da tanade-tanaden sashe na 84 (12) na 2022, wanda ya ci karo da tsohuwar dokar ta sashe na 137(1)(G) a kundin dokokin Nijeriya na 1999. Domin za su iya zama abin dogaro wajen hana ɗan takarar cigaba da burinsa na takarar wanda fadar shugaban ƙasa ta tsara za a gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu shekara ta 2023 mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *