2023: Na yafe wa Osinbajo, inji Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan takarar kujerar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce, ba shi da sauran damuwa a ransa game da Mataimakin Shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, yana mai cewa, ya yafe masa bisa takara da ya yi da shi a lokacin zaven fitar da gwani na jam’iyyar.

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya bayyana haka ne ranar Litinin lokacin da yake jawabi ga wata ƙungiyar da ta yi wa Osinbajo hidimar takarar shugaban ƙasa a Kano jawabi.

A cigaba da fafatawa a zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, an yi ta cece-kuce bayan da mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana ƙudirinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa tare da Tinubu.

Yayin da wasu ke iƙirarin bai dace Osinbajo ya yi takara da Tinubu, tsohon ubangidansa wanda ya tsayar da shi a matsayin abokin takarar Buhari a shekarar 2015 ba, inda wasu kuam ke ganin cewa Osinbajo na da ’yancin tsaya wa takara kamar yadda tsarin mulkin ƙasa ya ba da dama.

Daga ƙarshe, Bola Tinubu ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar inda ya samu ƙuri’u 1271 inda ya doke manyan abokan hamayyarsa, mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, da tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi.

Da ya ke magana a ranar Litinin game da batun a karon farko a bainar jama’a, Tinubu ya ce, babu wata matsala tsakaninsa da mataimakin shugaban ƙasa, kuma ya yafe masa.
“Ba ni da komai a kansa. Na je gidansa bayan kammala zaɓen fidda gwani,” inji Tinubu.

A halin da ake ciki, Yemi Osinbajo ya umurci dukkan ma’aikatan ofishinsa waɗanda ke cikin jam’iyyar APC, Majalisar Kamfen ɗin Shugaban Ƙasa, PCC, da su ba ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu iyakar ƙoƙarinsu.

Osinbajo ya bayar da umarnin ne a wata ganawa da ma’aikatan sa waɗanda ke cikin kwamitin na PCC.

Da ya ke bayyana hakan, mai taimaka wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Ajuri Ngelale, ya ce, Osinbajo ya jaddada muhimmancin aikin.

Ngelale, wanda yana ɗaya daga cikin mai magana da yawun ƙungiyar yaƙin neman zacen Tinubu-Shettima, ya ce, mataimakin shugaban ƙasar ya yi kira ga waɗanda abin ya shafa da su gudanar da ayyukansu ba tare da tsangwama ba.

Ya kuma buƙaci jama’a da su yi watsi da duk wani bayani da ke nuna akasin haka.