Hukumar Zakka da Waƙafi ta Sakkwato ta raba tallafi da kayan gwamnati a Yabo

Spread the love

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

A cigaba da raba zakkar da aka tara a gundumomi da kuma raba kayan Gwamnatin Jihar Sakkwato. A ranar Talata, Shugaban Zartarwar Hukumar Malam Muhammad Lawal Maidoki (Sadaukin Sakkwato), ya jagoranci ƙaddamar da rabon kayan gwamnatin jiha da suka haɗa buhunan abinci guda 100 da kuɗi rabin miliyan tare da kayan sallah ga marayu 100 da kuɗin ɗinki Naira 100,000 ga marayun yankin, tare da raba zakkar da gundumar ta tara ta dabbobi, abinci da kuɗi.

Shugaban ya yaba wa gundumar kan wannan ƙoƙarin, kana ya yi kira a gare su da su dage da wannan riƙe kambin da suka jima da shi wajen tara zakka. Ya yi kira a gare su da su tashi tsaye, wajen neman ilimi na addini da zamani, sana’a da kula da tarbiyyar matasa. 

Ya bayyana tallafin Gwamnatin Jihar Sakkwato zai game sunayen marayu 100 da aka zaƙulo cikin waɗanda gundumar ta kai wa hukumar, tare da na mabuƙata 100 da za su amfana da kuɗi da abinci don yin sallah cikin yanayi mai kyau.

Ya bayyana shirin hukumar na haɓaka noman itatuwan dabino a ɗaukacin jihar, ya bada tallafin itatuwan dabino domin raba wa masu buƙata. 

Sadaukin Sakkwato ya yi kira ga telolin yankin da suma su bada tasu gjdunmuwa ta hanyar tabbatar da an yi wa marayun ɗinkin sallah kuma a yi masu sauƙi idan har ba za su samu yi kyauta ba. 

Ya yi kira da a yi wa gwamnati da sauran shugabanni addu’a da duk mai hannu cikin wannan aikin.        

Taron ya samu halartar masu sanya ido daga wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu, kare haƙƙin bil adama, masu kiran kafafen watsa labarai, da shugaban majalisar Izala na ƙasa ɓangaren Jos Sheikh Nasiru Abdulmuhyi, wanda ya zo Sakkwato don gabatar da Tafsir na shekara-shekara, ya kasance babban baƙo da ya gabatar da nasiha a wajen, inda ya yi kira ga al’ummar yankin da su cigaba da aiwatar da wannan ƙoƙarin, kana su gode wa shugabannin su kuma yi masu addu’a.

Tun daga farko, sai da uban ƙasar, Sarkin Kabin Yabo, ya bayyana kayan da suka tara na zakka da suka haɗa da kuɗi kusan Naira miliyan 4 , raƙumi ɗaya da awaki da tumaki gami da buhunan abinci 282.

Sarkin Kabin Yabo ya kuma yi addu’a da godiya ga mahalarta taron da waɗanda suka bada zakkar.

By Editor