Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi
Tsohon gwamnan mulkin soji na Jihar Kaduna, Kanal Abubakar Ɗangiwa Umar (ritaya), ya miƙa kokensa na bara ga al’ummomin duniya, musamman kwamitin ƙasa da ƙasa ta ‘Red Cross’ (ICRC) da ta taimaka ta shiga cikin shawarwari na wakilci da zummar ceto fasinjoji dake cikin jirgin ƙasa wanda yau kimanin wata guda kenan yana kan hanyar sa zuwa garin Kaduna ‘yan ta’adda suka yi masa farmaki.
Wannan kira na tsohon gwamnan, ya biyo bayan kasancewar sa dangi kuma ɗan uwa ga wasu daga cikin fasinjojin jirgin ƙasan da aka kai wa farmaki, kamar yadda ya zayyana wa mai bai wa shugaban ƙasa shawara akan lamuran tsaro cikin takardar da ya rubuta masa, yana buƙatar a sakar masu ‘yan uwa.
Fafutukar dai tana zuwa ne yayin da mai magana da yawun waɗanda ake yin garkuwa da su, Dokta Abdullahi Jimoh a ranar Laraba da ta gabata ya shaida wa manema labarai cewar, har zuwa lokacin da yake yi masu jawabi, Gwamnatin Tarayya ba ta ce da su uffan ba dangane da shawarwari dake gudana tsakanin ta da ‘yan ta’addan kan buqatar sakin kamammun.
Ɗangiwa Umar, wanda shugaba ne na wata gungun sa kai mai laƙabin ‘Movement for Unity and Progress’ ya yi kiran neman taimakon ne a ranar Laraba da ta gabata, yana mai cewar, ya kaɗu matuƙa gaya yayin da ya kalli hotunan waɗanda aka yi garkuwan da su akan kafofin yaɗa labarai na jama’a.
Ya ce, “hotunan suna da matuƙar tayar da hankula, domin suna yin nuni ne ga hotunan mata da yaro da suka tagayyara, kuma suke cikin matsanancin yanayi na wahala.
“Ina mai gabatar da koke na wa Gwamnatin Tarayya ta matsa ƙaimi wajen ganin ta gaggauta ceto waɗannan bayin Allah da suke cikin halin ni’yasu.
“Ina kuma ƙara yin kira ga al’ummomin duniya, musamman kwamitin ‘Red Cross’ na duniya (ICRC) da ya taimaka shiga cikin shawarwarin na ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.
“Allah ya tirsasa zuciyoyin waɗannan ‘yan ta’adda ta yadda za su tausaya wa waɗanda suka yi garkuwa da su”, amin.
Wata kamammiyya da take da juna na kimanin watanni takwas yayin da aka yi garkuwa da su na fasinjojin jirgin ƙasan, an ce ta haihu lafiya. Macen, tana daga cikin mata guda biyu masu ciki a lokacin da lamarin ya faru.
Wannan mata an ce ta haihu lami-lafiya makon da ya gabata, yayin da ‘yan ta’addan suke nemi gudummawar jami’in kiwon lafiya zuwa dabar ta su, amma ba a san halin lafiyar abinda ta haifa ba.
