NLC za ta shiga yajin aiki na ƙasa don nuna goyon baya ga ASUU

Spread the love

Daga AMINA YUSUF ALI

Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta yi wa gwwmnati kashedin cewa, za ta shiga yajin aiki na ƙasa, har tsahon kwanaki uku, idan har Twamnatin Tarayyar ba ta daina yin buris da buƙatun ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ba.

Hakan yana ƙunshe ne a wata takardar bayani da kwamitin tafiyar da ƙungiyar NLC ya wallafa bayan wani taron da suka gudanar a ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata a Abuja.

a cikin takardar mai ɗauke da sa hannun Shugaban NLC na ƙasa, Ayuba Wabba da na Sakatarenta ba ƙasa, Emmanuel Ugboaja, NLC ta bayyana cewa, ta ba da wa’adin kwanaki 21 kacal ga gwamnatin Tarayya don ta biya wa ASUU buƙatunsu ko ta fuskanci yajin aiki a dukkan ma’aikatunta na ƙasa gabaɗaya.

Da ma dai tun fiye da watanni biyu da suka wuce ƙungiyar ASUU da sauran ƙungiyoyin da suka shafi jami’o’i wanda suka haɗa da ƙungiyar ma’aikatan jam’o’i NASU da SSANU, da kuma NAAT suke cikin yajin aiki amma har yau gwamnatin Tarayya ba ta yi wani abu a kan buƙatun da suka bijiro mata da su ba.

Gwamnati ba ta ce komai ba duk kuwa da yajin aikin nasu ya tilasta rufe dukkan jami’o’i mallakar gwamnati da suke a ƙasar nan.

A cewar ƙungiyoyin, yajin aikin ya zama tilas a gare su tunda gwamnatin Tarayya ta sa qafa ta Shure dukkan ɗimbin alƙawurra da yarjejeniyar da suka yi tsakaninsu da ita.

A taron da suka yi ranar Alhamis ɗin da ta gabata a Abuja, kwamitin tafiyar da ƙungiyar NLC sun bayyana cewa, za su tafi yajin aikin na kwana uku ne bayan sun ba da wa’adin kwanaki uku ga gwamnati don tuna mata cewa, Jami’o’i da sun jima da yawa a rufe.

Da ma dai an daɗe ana sa-toka, sa-katsi tsakanin ƙungiyar Malaman jami’ar da gwamnatin Tarayya, amma har yau ba a samu biyan buƙatar da suka nema ba, shi ya sa har yau jami’o’in suke a rufe.

Tun a ranar 14 ga watan Fabrairu na 2022 ne dai ASUU suka ba da sanarwar tafiya yajin aiki na makwanni takwas saboda ƙin cika musu buƙatunsu da gwamnatin tarayya ba ta yi ba. Buƙatun sun haɗa da riƙe alawus-alawus ɗin malaman jami’a, biyan malamai ta tsarin da suka zaɓa, da sauransu.

Amma har yanzu gwamnati ba ta yi wani yunƙuri ba. Shi ya sa suka cigaba da yajin aikin maimakon su dakatar da shi ranar 14 ga Maris kamar yadda suka ba da sanarwar

By Editor