Zan bada gudunmuwa wajen kawo cigaban ‘yan Arewa mazauna Legas – Hajiya Amina

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Shugabar mata ta ƙungiyar ‘Arewa Community’ da ke jagorantar shiyya yammacin Legas, Hajiya Amina ta sha alwashin yin iyakacin ƙoƙarinta tare da bada gudunmuwa wajen kawo cigaba mai ma’ana ga al’ummar Arewacin Nijeriya mazauna Jihar Legas.

Hajiya Amina ta tabbatar da hakan ne yayin ziyarar gaisuwar azumi da ta kai wa shugaban ƙungiyar na jihar, Alhaji Sa’adu Yusuf Dandare Gulma a ofishin sa ranar Lahadin da ta gabata.

Ta ce za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin ta haɗa kan al’ummar shiyyar da take shugabanta, musamman wajen kawo zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin su da sauran ƙabilu mazauna jihar ta Legas.

 A nasa ɓangaren, shugaban ƙungiyar, Alhaji Sa’adu Dandare Gulma ya nuna matuƙar jin daɗinsa da wannan ziyara da Hajiya Amina ita da tawagarta suka kawo masa, inda ya ƙara bata shawarwarin yadda za ta cigaba da mu’amala da ‘ya’yan ƙungiyar da ma sauran jama’a baki ɗaya.

Kazalika, Alhaji Yusuf ya horeta da ta kasance mai haɗa kawunan ‘ya’yan ƙungiyar da kuma zama da kowace ƙabila lafiya ba tare da nuna ƙabilanci ba ko bambancin addini ba.

Da ƙarshe, Hajiya Amina ta nuna farin cikinta da kuma yin godiya ga shugaban ƙungiyar da ya bata wannan wakilci na shiyyar yammacin Legas.

Sannan ta yi addu’ar samun zaman lafiya a Nijeriya baki ɗaya, da fatan Allah ya sa a yi shagulgulan ƙaramar sallah lafiya.

By Editor