A ranar Juma’a Kotun Ƙoli ta kori ƙarar da tsagin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya shigar yana mai neman kotu ta tabbatar da shi a matsayin halastaccen APC na jihar Kano bisa ga tsagin Gwamna Abdullahi Ganduje.
Kotun ta ce ƙarar da ɓangaren Shekarau ya shigar ba ta da hurumin da kotu za ta saurare ta, don haka ta kori ƙarar sannan ta tabbatar da tsagin Gwamna Ganduje a matsayin halastaccen APC a Kano.
Cikkaken labari na nan tafe….
