Zan iya cigaba da zama kocin Madrid shekaru 10 – Ancelotti

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya bayyana cewa, wataƙila ya yi ritaya idan ya bar ƙungiyar da ta zama zakarar gasar La Liga a bana, sai dai ya ce, a shirye ya ke ya cigaba da zama tare da qungiyar Madrid ɗin tsawon shekaru masu yawa a nan gaba.

Ancelotti ɗan ƙasar Italiya mai shekaru 62 a duniya, ya zama koci na farko a tarihi da ya lashe kofunan manyan lig-lig guda biyar na Turai, nasarar da ya cimma a wannan kakar tare da Real Madrid bayan lashe gasar La Liga, inda kuma ya jagoranci karawa da Manchester City ranar Laraba a gasar kofin Zakarun Turai.

Yanzu haka dai Kocin ɗan ƙasar Italiya yana yarjejeniya da Real Madrid har zuwa shekarar 2024, bayan da ya koma ƙungiyar a karo na biyu a shekarar bara daga ƙungiyar Everton.

Yayin wata zantawa da manema labarai ne kuma, Ancelotti ya ce, zai iya cigaba da horar da Real Madrid tsawon shekaru 10, idan ƙungiyar ta buƙaci hakan.

A ranar Laraba ne Real Madrid da Manchester City suka sake haɗuwa a Santiago Bernabeau domin buga zagaye na biyu.

Koda yake Manchester City da farko ta lallasa Real Madrid da ƙwallaye 4-3. Amma daga baya Real Madrid ta ramuwa  da ci 3-1.

Tuni kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya bayyana cewa, dole ta sa ya ɗauki kasada a wasan maƙutar suna son samun nasara akan Manchester City.