Ranar Dimokuraɗiyya: Gwamnati ta ba da hutun gama-gari

Spread the love

Daga WAKILINMU

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 13 ga Yunin 2022 a matsayin ranar hutun gama-gari albarkacin Bikin Ranar Dimokuraɗiyya.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a Abuja.

Ministan ya yi amfani da wannan dama wajen taya ‘yan Najeriya murna dangane da bikin wannan rana, tare da yin kira ga ‘yan kasa baki ɗaya da a ci gaba da mara wa gwamnati baya don tabbatar da ingancin ƙasa a dukkanin fannoni.

“Yayin da muke bikin Ranar Dimokuraɗiyya, ya kamata mu waiwaya mu dubi ƙoƙarin magabatanmu sannan mutabbatar da Najeriya ta ci gaba da zama kasa dunƙulalliya, mai hadin kai kuma mai tsaro da zaman lafiya.

“Duba da ƙalubalen da muke fuskanta yau a Najeriya, kada hakan ya sa mu rarraba, face mu so juna da gaskiya ta yadda za mu fahimci juna da girmamawa sannan mu zauna tare cikin lumana,” inji Aregbesola

Daga nan, Ministan ya shawarci ‘yan Najeriya da su yi amfani da sabuwar manhajar nan ta tsaro da aka ƙaddamar kwanan nan, wato ‘N-Alert’ a taƙaice domin yaƙi da matsalar tsaro da sauransu.

Kazalika, ya ba da tabbacin Najeriya za ta ci gaba da bunƙasa duba da irin ƙoƙarin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi wajen daidaita lamurran ƙasa.

By Editor