Daga ABBA YAKUBU ABDULLAHI
Wani muhimmin batu da ya sake kunno kai a fagen siyasar ƙasar nan shi ne batun ɓacewar takardun shaidar karatun wasu ’yan siyasa masu neman manyan muqamai a ƙasar nan. Labari na baya bayan nan shi ne na sanarwar ɓacewar takardun shaidar kammala makarantar firamare da sakandire na mataimakin ɗan takara na wucin gadi ga Bola Ahmed Tinubu wanda Jam’iyyar APC ta tsayar domin ya yi mata takarar shugaban ƙasa.
Rahotanni na bayyana cewa, Kabir Ibrahim Masari wanda aka gabatar da sunan sa a matsayin mataimakin Tinubu, ya shaida wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta INEC cewa takardun makarantar sa sun ɓata. Wannan na zuwa ne a yayin da ’yan Nijeriya ke cigaba da muhawara kan batun ɓacewar takardun karatun shi kansa Jagaban Bola Ahmed Tinubu, da ya yi ikirarin takardun sun ɓace ne bayan tafiyar sa gudun hijira a shekarar 1994, lokacin yana cikin manyan jiga jigan ƙungiyar NADECO, da suka yaƙi tsohuwar gwamnatin mulkin soja ta marigayi Janar Sani Abacha, don neman a koma amfani da tsarin Dimukraɗiyya.
Batun takardun shaidar karatun ’yan siyasa ya daɗe yana jawo cece kuce musamman a idan aka ce kakar zaɓe ta matso. Na san ya yi wuri ‘yan Nijeriya su manta da dambarwar da ta tashi a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a shekarar 2015 inda aka tada qura kan cewa, shugaba Buhari wanda a lokacin ya ke takarar neman shugabancin ƙasar nan a karo na uku, cewar ba shi da takardar shaidar kammala makarantar sakandire, zargin da shugaban ƙasar ya musanta kuma ya haƙiƙance kan cewa ya kammala karatunsa a na sakandire a makarantar Provincial ta Katsina a shekarar 1961 tare da wasu manyan ƙasa, kuma akwai hujjar hakan a wajen rundunar sojojin Nijeriya, inda ya yi aikin soja.
Wannan taƙaddama ta yi ta jawo ruɗani da zarge-zarge musamman daga ‘yan kudancin ƙasar nan da abokan adawar siyasa, waɗanda suka riqa nuna rashin cancanta da dacewar barin mutumin da ba shi da cikakkun takardun makaranta ya shugabanci ƙasar nan.
Ko da ya ke tsari ne na dokar ƙasa ya zama duk wanda zai yi takarar wani muƙamin siyasa a Nijeriya lallai ya samu shaidar karatu daga wata makaranta da doka ta amince da ita. Wanda hakan ne zai tabbatar wa da ‘yan ƙasa cewa, yana da ilimi da cancantar da zai iya shugabanci kuma ya wakilci ƙasa a ko’ina a duniya ba tare da wata fargaba ba. Sai dai shin wanne tanadi doka ta yi game da haka? Kuma shin me al’ummar ƙasa suke buƙata ne daga shugabannin da za su mulke su? Adalci da iya tafiyar da mulki ne ko yawan takardun makaranta da gogewa a Turanci?
Sashi na 131 sakin layi na (d) da sashi na 177 shi ma a sakin layi na (d) na kundin tsarin mulkin ƙasa na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima sun yi bayanin ƙa’idojin da ake buƙata na tsayawa takarar Shugaban Ƙasa da na Gwamna da ya shafi shaidar takardun makaranta ko madadinsu. Sai dai sashi na 137 da 182 bai fito ƙarara ya nuna lallai ana magana ne a kan shaidar takardun karatu na makaranta ake nufi ba, waɗanda rashin su zai iya sa Shugaban Ƙasa ko Gwamna ya rasa kujerarsa.
Abin da sashi na 131 na kundin tsarin mulkin ƙasa ya buƙata game da mai neman takarar Shugaban Ƙasa shi ne: (a) lallai ne ya zama ɗan ƙasa wanda aka haife shi a cikin Nijeriya, (b) lallai ya zama ya kai shekaru arba’in da haihuwa, (c) lallai ya zama yana takara ne ƙarƙashin wata jam’iyyar siyasa kuma jam’iyyar ta san da takararsa, (d) lallai ya zama ya yi makaranta ko wata shaida makamanciyar haka.
Wannan shekara ta shaidar kammala karatu ita ce aka fassara ta a sashi na 318, inda aka yi nuni da cewa, (a) lallai ana buƙatar ya zama yana da shaidar kammala karatun sakandire ko makamanciyar haka, ko shaidar karatun malanta na Grade ll (b) ya zama a qalla ya yi karatu zuwa matakin sakandire ko (c) shaidar kammala aji shida na makarantar firamare ko makamanciyarta, (i) sannan ana son ya zama ya taɓa yin wani aiki a ƙarƙashin wata hukuma da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta amince da ita a cikin ƙasa na tsawon shekaru goma, (ii) ya zama ya halarci wasu kwasa kwasai na samun horo a wasu cibiyoyin ilimi da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta amince da su, sannan adadin zuwan kwasa-kwasan ya zama idan an haɗa kwanakin za su kai kamar na shekara guda, kuma (iii) ya zama ya iya karatu da rubutu, yana iya fahimtar Turanci yadda Hukumar Zave ta Ƙasa ta gamsu da shi, sannan (d) ana son ya zama yana da wata shaidar karatu da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta amince da ita.
Wannan yana nuna akwai zavi da aka bai wa mai tsayawa takara na shaidar da za ta ba shi ‘yancin shiga takara da neman amincewar ’yan ƙasa. Wasu masana shari’a na ganin nacewa da sa ido kan takardun shaidar kammala makaranta, ba shi ne muhimmin abin da ya kamata a fi mayar da hankali a kai ba, amma abin nazari da dubawa shi ne wacce gudunmawa mutum zai bayar wajen gina ƙasa da kawo sauyi a rayuwar ’yan Nijeriya?
Mai yiwuwa mai karatu zai tuna da tsohon Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya a Jamhuriya ta huɗu, Salisu Buhari, wanda aka sauke daga kujerarsa sakamakon ƙaryar da ya yi a takardunsa na makaranta, wanda a baya ya nuna ya kammala karatunsa na Jami’a a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, amma bincike ya nuna cewa bai kammala ba korarsa aka yi, kuma bai yi aikin hidimar ƙasa na NYSC ba. Sannan ya yi ƙarya a shekarunsa, inda ya ce, shekarunsa a lokacin 36, amma daga bisani aka gano asalin shekarunsa ba su kai 30 ba. Bayan ƙaryar cewa ya yi wani karatun ilimin kasuwanci a Jami’ar Toronto da ke ƙasar Kanada.
Wannan ya ja masa rasa kujerarsa, duk kuwa da yadda ya yi farin jini da karvuwa a wajen ’yan Nijeriya, kasancewar sa matashi kuma mutum na huɗu a manyan ƙasar nan. Amma saboda ƙaryar takardun makaranta, ya jawo lalacewar siyasarsa, da zubewar kimarsa a idon ’yan ƙasa.
Ba Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, tsohon Kakakin Majalisa Salisu Buhari, tsohon Gwamnan Jihar Legas Bola Ahmed Tinubu ko abokin takararsa na Babban Zaɓen 2023 Kabir Ibrahim Masari ne suka taɓa samun wannan matsala da take neman ɓata musu suna da siyasa ba hatta tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo sai da ya yi zargin cewa digiri na biyu da ake cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya samu shi ma ba gaskiya ba ne. Kuma binciken ’yan jarida ya kasa tabbatar da akasin haka, domin kuwa Jami’ar da aka ce ya samu digirinsa na PhD wato Jami’ar Fatakwal ba ta iya ba da shaidar lallai ya kammala ba.
Tsohon shugaban Jam’iyyar APC kuma tsohon Gwamnan Jihar Edo Adams Oshiomhole shi ma a shekarar 2012 an yi masa zargin ƙarya a takardun makarantarsa, inda abokin karawarsa na Jam’iyyar PDP Janar Charles Airhiavbere mai ritaya ya yi zargin cewa makarantar firamare ta Iyamoh da Oshiomhole ya ce, ya shiga a shekarar 1957 ya kammala a 1962 ba gaskiya ba ne. Domin kuwa, Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Edo ta tabbatar da cewa, sai a shekarar 1963 ne ma aka buxe makarantar.
Ƙaryar takardun karatu ba sabon abu ba ne a Nijeriya, wani abin kunya ne da zubewar mutunci, musamman ga ’yan siyasa da manyan masu riƙe da muqaman gwamnati, waɗanda ’yan Nijeriya ke ganin yawan iliminsu shaida ce da ke nuna za su yi rawar gani wajen tafiyar da mulkin ƙasar nan, idan aka ba su dama.
Irin waɗannan ƙarairayi da ake samu a wajen ’yan siyasar mu babban abin kunya ne da zubar da darajar ilimi. Wanda a ƙarshe ke zubar wa mutum kima da lalata martabar siyasarsa. Sannan lallai ne mahukunta a ƙasar nan su ɗauki alhakin wayar wa ’yan ƙasa kai muhimmancin tsare gaskiya da duba cancanta wajen ɗan takara ba ƙwarewarsa a Turanci ko tarin takardun makarantar da ya ke da su ba. Domin yadda ake wasa da hankalin ’yan Nijeriya idan lokacin siyasa ya gabato abu ne da ya ke karayar da zuciyar ’yan Nijeriya.
Ɗan Nijeriya ba ya buƙatar sai wani ya gaya masa cewa, laifi ne mai girma a dokar ƙasa wani ya shirya takardun bogi don ya samu mulki ko ya hau wata kujera. Kuma shaida ce da ke tabbatar da cewa, duk ɗan siyasar da ke yin haka ba lallai ne ya zama shugaba nagari ba. Irin su ne ake samu da shirya almundahana da rashin gaskiya, saboda dama abin da ya fi ƙwarewa a kai kenan.
Allah ya ba mu shugabanni nagari masu kishin talakawa da son cigaban ƙasa, ko da ba su da manyan takardun shaidar kammala makaranta. Shugaba mai gaskiya da adalci ya fi ɗan siyasa mayaudari da mai son kansa.
