’Yan bindiga sun kai wa tawagar Shugaba Buhari hari a Katsina, sun jikkata biyu

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wasu gungun ’yan bindiga sun buɗe wuta kan ayarin motocin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da aka tura domin tattaki zuwa Daura, jihar Katsina domin gudanar da bukukuwan Sallah a ranar Talata.

Da ya ke mayar da martani ga wannan lamari a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai, mai taimaka wa Shugaban Ƙasa, Garba Shehu ya yaba wa jami’an tsaron Fadar Shugaban Ƙasa kan nasarar daƙile harin.

“Fadar shugaban ƙasa ta bayyana harin a matsayin abin baƙin ciki da rashin jin daɗi, lamarin harbin da ya faru a kusa da Dutsinma, jihar Katsina, a kan ayarin motocin da ke ɗauke da jami’an tsaron shugaban ƙasa na Advance Team, Protocol da kuma jami’an yaɗa labarai gabanin tafiyar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari zuwa Daura domin yin Sallah.”

“Maharan sun buɗe wa ayarin motocin wuta ne daga inda suka yi musu kwanton ɓauna amma sojoji da ’yan sanda da jami’an DSS da ke tare da ayarin sun daƙile harin.”

“Mutane biyu da ke cikin ayarin motocin suna karɓar magani kan ƙananan raunukan da suka samu. Duk sauran ma’aikata da ababen hawa sun isa Daura lafiya,” inji sanarwar.

By Editor