Yadda PDP ta lallasa APC a zaɓen Osun

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗan takarar gwamnan Jihar Osun a ƙarƙashin Jam’iyyar People Democratic Party (PDP), Sanata Ademola Adeleke ya laahe zaɓe a ƙananan hukumomi 17 a cikin 30 da ke Jihar Osun.

Ya lallasa abokin karawarsa na Jam’iyyar All Progressive Congress (APC), kuma gwamnan jihar na yanzu, Adegboyega Oyetola wanda ya samu nasarar cin ƙananan hukumomi 13.

Ga dai yadda sakamakon zaɓen gwamnan ya kasance kamar yadda Hukumar INEC ta bayyana a ranar Asabar 16 ga Yuli, 2022.

Ƙaramar Hukumar Boluwaduro
APC – 5,649
PDP – 5,860
Dr. Kehinde Bolarinwa

Ƙaramar Hukumar ILESA ta Gabas
APC – 13,452
PDP – 10,969
Farfesa Adepoju Tejumaye

Ƙaramar Hukumar OSOGBO
APC – 22,952
PDP – 30,401
Farfesa Musa Obalola

Ƙaramar Hukumar ILA
APC – 11,163
PDP – 13,036
Farfesa Aderonke Samuel

Ƙaramar Hukumar IFE ta Tsakiya
APC 17,880
PDP – 13,532
Farfesa J. A. Adewara

Ƙaramar Hukumar IREPODUN
APC – 12,122
PDP – 14,369
Dr. Omobolanle Ademilua

Ƙaramar Hukumar ORIADE
APC – 14,189
PDP – 15,947
Farfesa Sunday Adebisi

Ƙaramar Hukumar AYEDAADE
APC – 14,527
PDP – 13,380
Dr. Johnson Agunsoye

Ƙaramar Hukumar OLAOLUWA
APC – 9,123
PDP – 7,205
Farfesa Sunday Ojolo

Ƙaramar Hukumar IWO
APC – 17,421
PDP – 16,914
Prof Khalid Adekoya

Ƙaramar Hukumar EDE ta Kudu
APC – 5,704
PDP – 19,438
Dr. Olayinka Agunloye

Ƙaramar Hukumar ISOKAN
APC – 10,833
PDP – 10,777
Dr. Bamidele Samuel

Ƙaramar Hukumar IREWOLE
APC – 18,198
PDP – 14,216
Farfesa Lukman Adams

Ƙaramar Hukumar EJIGBO
APC – 14,355
PDP – 18,065

Ƙaramar Hukumar EDE ta Arewa
APC – 9,603
PDP – 23,931
Farfesa Abayomi Okanlawon

Ƙaramar Hukumar EGBEDORE
APC – 9,228
PDP – 13,230
Dr. Babatunde Alade

Ƙaramar Hukumar ATAKUMOSA ta Gabas
APC – 7,449
PDP – 6,992
Farfesa Oludiran Akinleye

Ƙaramar Hukumar IFE ta Kudu
APC – 12,481
PDP – 9,116
Dr. Oluwafemi

Ƙaramar Hukumar IFE ta Gabas
APC – 19,353
PDP – 18,071
Farfesa Amuda

Ɗan takarar Jam’iyyar PDP, Sanata Ademola Adeleke shi ne ya lashe zaɓen jihar da ya gudana Asabar da ta gabata da zunzurutun ƙuri’u 403,371.

Sai abokin takararsa kuma Gwamnan jihar da ke kai na Jam’iyyar APC, Adegboyega Oyetola da ya samu ƙuri’u 357,027, inda Sanata Adeleke ya lashe zaɓen da tazarar ƙuri’u 28,344.

Sai kuma ɗan takarar Jam’iyyar ADP, Kehinde Atanda wanda ya zo na uku da ƙuri’u 10,104.

Baturen zaɓe kuma Shugaban Jami’ar Legas, Farfesa Oluwatoyin Temitayo Ogundipe ya bayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen a dokance.

Ga yadda sakamakon ƙarshe na zaɓen ‘yan takarkarar gwamnan jihar da ya gudana ranar Asabar ya kasance.

A – 4,515
AAC – 2148
ADP – 10,104
APC. 375,027
APM – 1,222
APP – 601
BP- 374
LP 2,729
NNPP – 393
NRM – 777
PDP – 403,371
PRP -1007
SDP – 515
YPP – 1,303
ZLP – 364

By Editor