Shugaba Xi ya taya Ƙasar Masar murnar cika shekaru 70 da kafuwarta

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da saƙon taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar ƙasar Masar, ga takwaransa na Masar ɗin Abdel-Fattah al-Sisi.

Cikin saƙon wanda ya aike a Asabar ɗin nan, shugaba Xi ya ce Masar ta ci gaba da bin hanyar nasara bayan samun ‘yancin kai, ta kuma samu bunƙasuwa, tare da taka muhimmiyar rawa a harkokin da suka shafi ƙasa da ƙasa da na shiyyoyi.

Shugaban na Sin, ya ce ƙasar sa na mayar da hankali matuƙa ga bunƙasa alakar ta da Masar.

Ya ce a shirye yake ya yi aiki tare da shugaba Al-Sisi, ta yadda sassan biyu za su mara wa juna baya, da ingiza nasarar shawarar nan ta “ziri ɗaya da hanya ɗaya”, tare da yin hadin gwiwa wajen aiwatar da shawarar ciyar da duniya gaba, da kare moriyar ƙasashe masu tasowa, da ƙara azama wajen gina al’ummar Sin da Masar mai makomar bai ɗaya a sabon zamani, ta yadda hakan zai amfani ƙasashen 2, da ma al’ummun su baki ɗaya.

Fassarawar Saminu Alhassan

By Editor