Shugabannin JKS da na Ƙasar sun karɓi allurar rigakafin COVID-19 wadda aka sarrafa a ƙasar

Daga CMG HAUSA

Mataimakin shugaban hukumar kiwon lafiya ta ƙasar Sin Zeng Yixin, ya ce shugabannin jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin, da jagororin ƙasar sun karɓi allurar rigakafin COVID-19 da aka sarrafa a cikin ƙasar.

Zeng ya bayyana hakan ne a Asabar din nan, yayin taron manema labarai na tsarin haɗin gwiwar kandagarki da shawo kan annoba na majalissar gudanarwar ƙasar Sin, yana mai cewa “Hakan ya nuna amincewar da rigakafin COVID-19 samfurin ƙasar Sin ya samu”.

Kazalika, ƙarin wasu shugabannin ƙasashen duniya sama da 30, sun karɓi rigakafin samfurin na ƙasar Sin.”

Jami’in ya ƙara da cewa, akwai nau’o’in rigakafin COVID-19 na Sin guda 3, waɗanda hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta amince da amfani da su a matakin gaggawa.

Haka nan, ya ce sama da ƙasashe 100 sun samu izinin amfani da nau’oin rigakafin, yayin da da yawa daga cikinsu suka amince da rigakafin ta Sin a matsayin wadda ake iya yiwa yara ƙanana.

A ƙasar Sin, an yi wa mutane kusan biliyan 1.3 rigakafin COVID-19. Adadin da ya kai kusan kaso 92.1 bisa ɗari na daukacin jama’ar ƙasar.

Kuma kimanin kaso 89.7 bisa ɗari na al’ummar kasar sun karɓi alluran karo 2, yayin da kaso 71.7 bisa dari suka karɓi ƙarin allurar a zagaye na 3.

Bugu da ƙari, ƙasar Sin na aiki domin samar da rigakafin COVID-19 samfurin Omicron.