Yunwa ba Dimukuraɗiyya ba ce

Daga BELLO WANG

Kamfanin watsa labarai na BBC, ya watsa wani labari a kwanan nan, wanda ke cewa jama’ar ƙasashen Larabawa, suna yanke ƙauna ga tsarin dimokuradiya irin na ƙasashen yamma.

A ganinsu, tsarin ya hana gwamnati taka rawa yadda ake bukata, a fannonin tabbatar da tsaro da raya tattalin arizki.

BBC ya watsa labarin ne, bisa rahoton da ƙungiyar binciken ra’ayin jama’a ta Arab Barometer ta gabatar, wanda Michael Robbins, shehun malami na jami’ar Princeton ta ƙasar Amurka, ya wallafa. Shi kuma wannan malami ya rubuta dalilin da ya sa Larabawa suke yanke kauna ga tsarin dimokuraɗiyya na ƙasashen yamma, wanda shi ne “mutane na fama da yunwa, suna buƙatar burodi.”

Cikin shekaru fiye da 10 da suka gabata, an yi jerin juyin juya hali na ɗaukar tsarin dimokuradiya a wasu ƙasashen Larabawa. Zuwa yanzu, ko an samu ci gaban harkoki a wadannan ƙasashe? Amsa ita ce A’a, ba a samu ba!

Idan mun ɗauki Tunisia, da Lebanon, da Iraƙi a matsayin misali, a duk waɗannan kasashe, an samu sabuwar gwamnati ta hanyar jefa kuri’a, kuma dukkansu sun ɗauki tsarin dimokuradiya irin na ƙasashen yamma. Amma zuwa yanzu, jimillar GDP kan kowane mutum a ƙasar Tunisia ta yi kasa, idan an kwatanta da na shekarar 2011.

Kana ƙasar Lebanon ma na fuskantar haɗarin rushewar tsarin hada-hadar kuɗi, yayin da ƙasar Iraƙi ke fama da matsalar rashin kwanciyar hankali.

Duk waɗannan abubuwa sun nuna cewa, tsarin dimokuraɗiyya na ƙasashen yamma, ba wani abu ne dake iya daidaita dukkan matsalolin da ake fuskanta ba.
Ban da ƙasashen Larabawa, ko a kasashen yamma, jama’a suna da cikakken imani game da tsarin dimokuraɗiyya irin nasu? Ko alama!

Tsohon ɗan majalisar dattawan Amurka Tom Daschle, ya rubuta wani bayani a kwanan baya, wanda aka wallafa shi a shafin yanar gizo na majalissun ƙasar Amurka, inda a ciki yake cewa, tsarin dimokuraɗiyya na kasar Amurka “yana daf da halaka kan sa”, sakamakon wasu manyan matsaloli da suka shafi zaman rayuwar jama’a, irinsu bambancin launin fata, da kisan gillar da ake yi da bindiga, da rashin daidaito a fannin samun kuɗin shiga, da hauhawar farashin kaya, da annobar COVID-19, da dai sauransu.

Haƙiƙa duk wata ƙasa na da irin nata al’adu, da yanayin kasa, waɗanda suka sha bamban da juna. Saboda haka, da wuya a ce akwai wani tsarin siyasa mafi kyau, wanda ya dace da kowa.

Da ma dai an gabatar da aƙidar Dimokuraɗiyya, don tabbatar da cewa gwamnati za ta yi kokarin kare haƙƙin jama’a ne, da biyan buƙatunsu. Idan ko burodi ma ba ta iya samar musu, ko rayuwa ta zama mai wuya a gare su, ke nan wannan “tsarin dimokuraɗiyya” ba na gaske ba ne.