Gwamnatin Bauchi ta keɓe kadada 200,000 don gudanar da ayyukan noman zamani

Spread the love

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Gwamnatin Jihar Bauchi ta bayyana buƙatarta na amincewa da wani kamfanin ƙwararru kan ayyukan gona mai laƙabin ‘Techgen Agro Consultants’ domin yin hidimomin raya ƙasa mai murabba’in kadada dubu ɗari biyu da aka keɓe domin gudanar da ayyukan noma na zamani a sassan jihar.

Gwamna Bala Mohammed ya ce wannan gagarumin shiri ya jiɓanci karɓar rancen kuɗi kimanin Naira biliyan hamsin daga Bankin Tarayyar Nijeriya (CBN) domin aiwatar da shirin bunƙasa ayyukan gona da aka yi wa laƙabi da ‘Accelerated Agricultural Development Scheme (AADS)’ wanda aka tsara shi domin ƙarfafa wa matasa ayyukan yi yadda za su yi tutiya da kyakkyawar rayuwa.

Gwamna Bala ya yi furucin ne yayin da yake ƙaddamar noman damina na wannan shekara ta 2022 da kuma buɗe kasuwar sayar da takin zamani waɗanda aka gudanar a garin Nabordo dake cikin ƙaramar hukumar Toro a ƙarshen makon nan, inda ya jaddada buqatar yin amfani da qarfi da qarfe domin cin gajiyar ɗimbin albarkatun gona da Allah ya huwace wa jihar domin bunƙasa tattalin arzikin jama’a.

Gwamnan sai ya yi waiwaye da cewar, gwamnatin jiha ta horas da matasa kimanin mutum 1, 000 kan aikace-aikacen gona, kiwon dabbobi, kifaye da tsuntsaye kamar kaji da sauransu, yana mai bayyana cewar, ta hannun kamfanin zuba jari (BIC) na jiha ne za a zuraro waɗannan maqudan kuɗaɗe na rance daga babban bankin tarayya domin bunƙasa ayyukan gona a jiha.

Ya bayyana cewar, shirin dungurungum ɗinsa zai kasance na kasuwanci ne da zummar bunƙasa tattalin arzikin manoman jiha, yayin da aka umarci ma’aikatar gona da albarkatun ƙasa, haɗi da kamfanin zuba jari na jiha su jajirce wajen tabbatuwar nasarar shirin a wannan jiha ta Bauchi.

Mohammed ya ƙara da cewar, gwamnatinsa ta ƙudira aniyyar bunƙasa sashin kiwon dabbobi la’akari da cewa ta ɗauki matakan tabbatar da lafiyar dabbobin kiwo, yayin da gwamnatin ta amince da yin amfani da kuɗaɗe Naira miliyan arba’in da huɗu wajen yi wa dabbobi allurar rigakafin kiwon lafiyar dabbobi a wannan shekara da muke ciki.

Ya kuma yi furucin cewar, gwamnatinsa za ta gina wani katafaren asibitin ƙwararru na kiwon lafiyar dabbobi a Ƙofar Ran dake cikin garin Bauchi, a yayin da kuma hukumar bunƙasa ayyukan gona ta BSADP take ƙoƙarin inganta hidimominta wa manoma domin zamanantar da ayyukan gona.

Gwamnan ya kuma bayyana vacin ransa bisa halayen wasu marasa kishi waɗanda suke gurɓata kayayyakin ayyukan gona da suka haɗa da takin zamani domin son zuciya na yin arziki dare ɗaya, yana mai cewa wannan hali ne na ɓatanci, kuma yana tabbatar da cewar, gwamnati za ta bi tsuwuiwiwar waɗannan ɓatagari domin yi masu hukuncin da ya dace.

Sanata Bala Mohammed sai ya umarci ma’aikatar ayyukan gona da ma’aikatar kula da ƙananan hukumomi da masarautu da su kafa wani kwamiti da gaggawa wanda zai ƙunshi jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki domin cafke da kuma yin hukunci ga waɗannan ɓatagari.

Ya bayar da tabbacin gwamnatin jiha za ta wadatar da taki da rahusan farashi, sa’annan sai ya ayyana farashin takin gwamnati ga mai saye akan: NPK Naira 15, 000, shi kuma Urea akan Naira 20, 500.

Gwamnan sai ya bayyana kadadar da noman damina da ake yi a kowace shekara da zummar azamar da manoma su duƙufa ka’in-da-na’in wajen noma wadataccen abinci da rungumar ayyukan gona a matsayin jigon tattalin arziki.

Mohammed ya ce gwamnatinsa da cibiyar inganci ta kwalejin fasaha da kimiyyar ta gwamnatin tarayya dake Bauchi sun rattava hannu akan wata yarjejjeniya ta horas da matasa akan dabarun ayyukan gona.

By Editor