A zahiri sai gwamnatin APC a Katsina ta ƙara azama wajen duba kura-kurai ta fuskar gyara ganin yadda gwamnatin Rt Hon His Exl. Alh Aminu Bello Masari ta ke daf da cika shekaru takwas tana mulki, inda wasu na yabo wasu na suka. An ce mutum ajizi ne.
Kuma iya ma mutane sai Allah amma a ce a na da hurumi na zaɓe sau uku ai ko shakka ban yi wanda zai fito ya kawar da gwamna Masari ban hango shi ba. Amsa ta ita ce ba gwamna Masari ba ɗaukacin gwamnonin APC a Arewa da Kudu duka su na aiki a jihohinsu.
Batun magance matsalolin tsaro a nan ma idan mun kula jama’a ta fi yayata matsala sama da idan nasara ce.
Tabbas ana fuskantar barazanar ’yan ta’adda musamman a jihohin Katsina da Zamfara, amma mu ƙara kula da kyau ko a watan jiya na Agusta a Katsina mun ga motocin yaƙi ma su sulke wanda Masari ya sawo domin tunkarar batun tsaro.
Haka a jihar Zamfara mu na jin dubaru na gwamna Matawalle na ba da damar iya mallakar bindigogi domin kare kai.
Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa. 07066434519/08080140820.
