Game da taron jin ta bakin ‘yan takarar Shugabancin Nijeriya guda uku

Spread the love

Daga BELLO MUHAMMAD SHARAƊA

Ranar Litinin 17 ga watan Oktoba 2022, aka yi zama na biyu a Arewa House da wasu mutum shida daga cikin masu neman shugabancin Najeriya a zaɓen shekarar zaɓe ta 2023.

An gayyaci Atiku Abubakar na PDP da Kola Abiola na PRP da Adewale na SDP a ranar Asabar. Dukkansu sun je kuma sun yi bayanin yadda za su tunkari matsalolin Arewa idan Allah ya ba su ragamar ƙasar nan.

A ranar an ware wa ɗan takarar shugabancin Nijeriya a jam’iyyar APC wato Alhaji Bola Ahmed Adekunle Tinubu da Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP su zo su baje nasu kolin yadda za su shawo kan manyan buqatun mutanen Arewa idan aka zave su. Tunde Rahman, amintaccen Tinubu a harkar labarai ya bada tabbas cewa Tinubu zai kasance a Arewa House don wannan taron.

Abin mamaki a ranar, sai ga wata zungureriyar takarda mai shafi uku daga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta hannun Abdulmumin Jibrin Kofa.

A cikin wannan takarda Rabi’u Musa Kwankwaso yana bada uzurin ba zai samu zuwa wannan zauren muhawara ba. Ya faɗi dalilansa: na farko,yana da uzuri na biyu bai gama kimtsawa ba, Na uku kuma a cewar sa, an shirya taron ne domin a biya buƙatar wani ɗan takara.

Ƙungiyoyi shida ne suka shirya wannan zaman su ne, Dandali tuntuba na ‘yan Arewa (ACF), Giduniyar Ahmadu Bello, Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), Arewa House, Jam’iyyar Matan Arewa, da Arewa Research and Development Project.

Na cika da mamakin wannan matsayin na Kwankwaso, kuma na daɗa nutsawa a cikin shakkun takarar Kwankwaso. Taruka uku masu muhimmanci Kwankwaso ya ƙauracewa.

An kira shi a taron Ƙungiyar lauyoyi ta Nijeriya (NBA), duk wani lauya yana cikin wannan ƙungiyar bai je ba. An kira shi taron LCCI duk wani ɗan kasuwar Nijeriya yana ciki, nan ma bai je ba. Waɗannan ƙungiyoyi guda shida su ne ƙashin bayan maganar Arewa, sun gayyace shi a Kaduna ma bai je ba.

Yarbawa suna da Afenifere da Yoruba Consultative Elders, Inyamurai suna da Ngdibo da Ohanaeze, mutanen Kudu maso kudu suna da IYC da NDF duk waɗannan ƙungiyoyi ƙungiyoyi ne masu ƙarfi, duk ɗan siyasa mai ƙarfi sai an gayyace shi dandamalinsu don ya gabatar da tunaninsa da manufarsa da yadda ya tsara daidaita lamura ba kuma da gangan ya noƙe. Dama ce babba ga wanda yake a shirye ba ɗan gangan ba.

Yanzu Kwankwaso yana nufin ba za shi taron muhawara da Nigerian Economic Summit Group NESG da hadin gwiwar Broadcasting Organisations of Nigeria, Nigeria Union of Journalists (NUJ), Nigeria Guild of Editors (NGE), Centre for Journalism Innovation and Development (CJID), Enough is Enough Nigeria (EiE), Budget and Radio, Television, Theatre and Arts Workers Union (RATTAWU) suka shirya a watan Nuwamba mai zuwa ba?

In kuwa haka ne, tun yanzu ya kamata Madugu ya koma kan shawarar da Salisu Yahaya Hotoro ya bayar cewa, ko dai ya zavi Abba, ya dawo gida Kano mai da hankali ya yi masa aiki, ko ya ɗauki talla da ɗawainiyar NNPP a Nijeriya, tsakiyarsa ta buɗe.

Muhammad Bello Sharaɗa, ɗan siyasa ne kuma mai saharho a kan lamurran siyasa.

By Editor