Daga AISHA ASAS
Masu iya magana na cewa, rana ba ta ƙarya, kuma duk nisan dare gari zai waye. Kamar yadda aka shelanta ranar Alhamis, 3 ga watan Nuwamba, 2022, a matsayin ranar da za a bayyana gwarazan fitacciyar gasar rubutu ta mata zalla da BBC Hausa ke shiryawa a kowacce shekara mai taken Hikayata. Cikin ikon Allah taron ya fara da misalin ƙarfe huɗu na yammacin ranar a ɗakin taro na ‘Yar Adua Centre da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.
An gabatar da gwarazan gasa da kuma matsayin kowacce daga cikin su, wato daga ta ɗaya har zuwa ta uku. Amira Souley wadda ta fito daga Maraɗi da ke Ƙasar Nijar ce ta lashe gasar inda ta zo na ɗaya, Hassana Ɗanlarabawa ta biyo bayanta a matsayin ta biyu, sai kuma Maryam Muhammad Sani da ta zama ta uku a gasar ta baya.
Jim kaɗan bayyana kammala taron, wakilin Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, ya tattauna da Maryam Muhammad Sani daga Jihar Kano wacce ita ta zo ta uku a gasar inda marubuciyar ta bayyana cewa, ta yi farin ciki marar misaltuwa. Amma da farko ta fara ne da gabatar da kanta.
“Sunana Maryam Muhammad Sani, haifaffiyar Jihar Kano ta Najeriya. Na yi karatu har zuwa matakin N.C.E. Ina da aure da yara uku. Na fara rubutu a shekarar 2019, na rubuta littattafai guda huɗu ban da gajerun labarai da ba za su ƙirgu ba.”
Maryam ta ci gaba da bayyana farin cikinta na zama ɗaya daga cikin waɗanda suka taka wannan matsayi. “Haƙiƙa kalaman bakina ba za su iya bayyana mizanin farin cikin da na tsinci kaina a ciki ba. Haƙiƙa wannan nasara ce daga Allah, ba don mun fi kowa iyawa ba, Allah ya ƙadarta mana wannan nasarar a rayuwarmu.”
Ta kuma ƙara da bayyana muhimmancin wannan gasa ta Hikayata ga marubuta masu tasowa, inda ta kira ta da gasar da ta yi zarra a tsakanin gasar rubutu da aka saba shiryawa, kasancewar ta wata dama ga marubutan da duniyar rubutu ba ta shelanta zuwan su, ta hanyar samun kujera a layin sanannu daga marubuta adabin Hausa.
“Haƙiƙa gasar Hikayata daban take da sauran gasanni. Gasa ce da ta cicciva marubuta da dama zuwa ga ƙololuwar nasara, ta kuma rabo su daga rarrafe a cikin duƙunan duhu zuwa ga haske. Marubuta sun bazama zuwa fafutukar neman ilimi don su kaifafa alƙaluman, da ke wakiltar tunaninsu.”
Da ta ke amsa tambayar ko ta taɓa shiga gasar a baya, Maryam ta shaida wa Manhaja cewa, “a shekarar da ta gabata na shiga gasar, amma ban yi nasara ba. A wannan shekarar sai na ƙara shiga, cikin ikon Allah na samu saƙon shigar labarina mai taken ‘Al’ummata’ cikin guda ashirin da biyar da aka fara tacewa a matakin farko.
Tamkar mafarki haka na ji, na shiga zulumi da fatan ina ma labarina ya shiga cikin guda sha biyu da BBC za su karrama da Satifiket. Kwatsam! Na samu waya daga gare su, Ina cikin marubuta uku da aka zavi labaransu.”
A ɓangaren Hassana wadda ita kuwa ta yi nasarar zuwa ta biyu, ita ma ta tattauna da jaridar Manhaja, inda ta fara da bayyana wa masu karatun mu ko ita wacece. “Sunana Hassana Labaran Ɗanlarabawa, haifaffiyar Jihar Kano a Najeriya, dagaa ƙaramar Hukumar Dala. Na yi makaranta daga matakin firamare har zuwa matakin N.C.E, inda na karanta Hausa da Ilimin addinin Musulunci. Ina da aure da yara biyu.”
Ta ci gaba da cewa,”Ni marubuciya ce, na rubuta litattafai kimanin guda tara zuwa goma, tare da gajerun labarai da dama, da kuma wasu labaran da na shiga gasa da su.”
Hassana ta bayyana wa Manhaja muhimmancin wannan gasa ta Hikayata a tata mahangar, inda ta ke cewa, “Gasar Hikayata ita ce uwa ga kowacce gasa da ake gabatarwa, musamman ga mata tun da gasar ta ta’allaqa ga su kaɗai. Gasar Hikayata ta ɗaga darajar marubuta mata sosai. Kuma kowacce marubuciya mace burinta a ce ta samu nasara a gasar Hikayata BBC.”
Ita kuwa Amira Souley wadda ta fito daga Jihar Maraɗi da ke Jamhuriyar Nijar, wacce kuma ta zama gwarzuwar gasar Hikayata ta bana, ta shaida wa Manhaja tarihinta a taƙaice da cewa, “ni haifaffiyar garin Maraɗi ce a Jamhuriyar Nijar, shekaruna ashirin da hudu. A cikin garin Maraɗi na yi dukkan karatuna na addini da na boko, inda a yanzu Ina koyarwa a wata firamare ta gwamnati. Na yi aure a 2015 ya rabu, bani da haihuwa ko ɗaya. Ni marubuciya ce, Ina alfahari da rubutu.”

Da ta ke amsa tambayar ko ta yi farin ciki da wannan nasara da ta samu, marubuciyar cewa ta yi, “Na yi matuƙar farin ciki a lokacin da na samu sako daga BBC cewa, labarina yana cikin labarai 25, farin cikin da ya haddasa mini fargaba da tashin hankali kasancewar shekarar da ta wuce ma labarina ya shiga cikin 25 din farko, wannan ya saka cikin zulumi da tsoro, saboda a baya labarina bai tava shiga cikin 3 farko ba, sai dai ya zo mataki na shida a cikin 12 da BBC Hausa suka karanta, wannan ne ya sa na rasa nutsuwa. Har sai da BBC Hausa suka sake kirana suka yi min wannan farin albishir cewa, Ina cikin gwaraza uku.
“Sai a lokacin na samu kwanciyar hankali, na yi farin ciki matuƙa wanda baki bai isa ya bayyana ba. Ubangiji ya yi hikima ɓoye abin da ke ƙasan zuciya shi ne kaɗai masanin adadin farin cikin da na yi, baki bai isa ya kiɗanye ba balle hannu ya rubuta. Alhamdulillah! ita ce kalmar da na fara furtawa lokacin da saƙon ya riske ni sannan na yi Raka’ata Shukur a madadin Sujudus Shukur.”
Wannan ita ce babbar ranar da marubuta adabin Hausa na Duniya ke ɗokin zuwanta, saboda muhimmancin ta ga cigaban adabi da bunƙasa harkar rubutun labaran hikayoyi. Gasar Hikayata da BBC Hausa ke shiryawa duk shekara ta zama madubin samun ɗaukaka da alfahari a wajen marubuta mata da ke ganin nasarar su ta kai wani babban mataki, da duniya ta shaida da basirarsu.
